Gwamna Abba Ya Yi Amfani da Damarsa, Zai ba Su Kwankwaso Mamaki a Zaben 2027
- Masanin siyasa, Abdulmalik Suleiman, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gina nasarorin gwamnatinsa kan gaskiya da rikon amana
- Ya ce hanyoyin da Gwamna Abba ya bi wajen gina mu'amala mai kyaua da jama'a, za su ba shi damar nasara a zabe mai zuwa
- Suleiman ya ce bin ka’idojin da suka dace, dakile almubazzaranci da kuma kashe kuɗi cikin taka-tsantsan sun dawo da amincewar jama’a kan gwamnatin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wani masani kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Abdulmalik Suleiman, ya ce gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gina nasarorin gwamnatinsa kan gaskiya, rikon amana da kyakkyawan mu'amala da jama’a.
Abdulmalik Suleiman ya bayyana hakan ne a Kano ranar Laraba, inda ya ce gwamnan ya yi imani da shugabanci mai tsari da kuma kare amanar da al’ummar jihar Kano suka ba shi.

Kara karanta wannan
Gwamnan Arewa ya je wurin Tinubu, ya fada masa abin da mutanen jiharsa za su yi a zaɓen 2027

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta rahoto Abdulmalik na bayyana hanyoyin da Gwamna Abba ya bi wajen sake gina amincewar jama'a da gwamnati a Kano.
Yadda Abba ya shiga zukatan jama'a
Ya bayyana cewa bin ƙa’idojin da suka dace, dakile hanyoyin satar kuɗaɗen gwamnati da kuma kashe kuɗi cikin taka-tsantsan da gwamnatin Abba ta yi sun dawo da amincewar jama’a.
Haka zalika, masanin ya ce wadannan hanyoyi da Abba Gida-Gida ya bi sun kuɓutar da albarkatun da za a yi amfani da su wajen zuba ayyukan ci gaba a jihar Kano.
Abdulmalik ya kawo ayyukan da aka gudanar a fannonin ilimi, kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa, da kuma biyan fansho da giratuti a kai a kai, a matsayin hujjojin ayyukan gwamnatin Kano.
Ya bayyana Gwamna Abba a matsayin jagora wajen goyon bayan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa zai iya kawo wa shugaban nasara a Kano a 2027 saboda kyakkyawar mu’amalar da yake da ita da mazauna jihar.

Kara karanta wannan
Allah mai iko: An gano babban bala'in da matuƙin jirgin sojoji ya kauce wa kafin ya yi hatsari
Ya ƙara da cewa farin jinin da ake ganin gwamnan yana da shi yana da alaƙa da abin da ya bayyana a matsayin cika alkawuran da gwamnatinsa ta yi wa al’ummar jihar.
Abin da Abba zai yi a zango na 2
Abdulmalik ya jaddada cewa wa’adin mulki na biyu ga Gwamna Abba zai ginu ne kan tubalin da aka riga aka kafa, yana mai bayyana hakan a matsayin wata dama ta ƙara ƙarfafa nasarorin da aka samu, bunƙasa da kuma ci gaban Kano.
Ya yi kira ga mazauna Kano da su ci gaba da bai wa gwamnatin goyon baya, yana mai cewa ci gaba da samun goyon bayansu zai ba ta damar cimma burinta na ci gaban jihar.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya gyara madatsar ruwa
Kun ji cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da madatsar ruwa ta Goron Dutse, bayan sama da shekaru 30 da wurin ya daina aiki.
Abba ya bayyana farfado da madatsar ruwan a matsayinNwani gagarumin tarihi ga jihar da kuma muhimmin mataki ga mazauna Kano da suka shafe tsawon lokaci suna fuskantar matsalolin samun ruwan sha.
Asali: Legit.ng