Tinubu na tsaka Mai Wuya, Jigon APC Ta Aika Wasika ga Shugaban Amurka kan Zaben 2027
- Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na APC, Timi Frank, ya roƙi Donald Trump da ya kawo dauki don tabbatar da sahihancin zaɓen Najeriya na 2027
- Ya buƙaci gwamnatin Amurka ta ƙarfafa ɗaukar mataki kan laifuffukan zaɓe tare da yin hulɗa da shugabannin siyasa da hukumomin zaɓe tun kafin zaɓen
- Frank ya ce tsaron masu zaɓe, hana jami’an tsaro nuna bangaranci da riƙon amana a shugabanci na da muhimmanci wajen tabbatar da sahihin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na ƙasa na APC, Timi Frank, ya rubuta tare da aika korafi shugaban Amurka, Donald Trump kan zaben Najeriya na 2027.
Jigon APC ya roƙi Shugaban Amurka Donald Trump da ya goyi baya kuma ya kawo dauki ta hanyar diflomasiyya da nufin tabbatar da sahihin babban zaɓen Najeriya na 2027.

Source: Facebook
Timi Frank ya nemi taimakon Amurka
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Frank ya bayyana haka ne a cikin wata wasiƙa mai taken “Ba Za a Samu Halastacciyar Nasara Ta Hanyar Maguɗi ba: Zaɓen 2027."
Timi Frank ya buƙaci gwamnatin Amurka ta goyi bayan matakan da za su inganta sahihancin zaɓe, ciki har da ƙarfafa ɗaukar mataki kan laifuffukan zaɓe.
Ya kuma yi kira da a fara tattaunawa da shugabannin siyasar Najeriya da hukumomin zaɓe tun kafin zaɓen domin ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin zaɓe.
Jigon APC ya bayyana damuwarsa
Frank ya nuna damuwa kan yadda jama’a ke kallon Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa fara hulɗar diflomasiyya tun da wuri zai taimaka wajen gina amincewa da tsarin zaɓe kafin ranar kaɗa ƙuri’a.
Ya ce:
“Lokacin ɗaukar mataki shi ne kafin zaɓe, ba bayan an kammala shi ba,” inda ya buƙaci a ɗauki matakan da za su taimaka wajen tabbatar da sahihancin zaɓe tun da wuri.

Kara karanta wannan
Ya mutane za su samu fetur mai araha a garuruwan da babu gidan man NNPC? An aika sako ga Tinubu
Ya roƙi gwamnatin Amurka da ta duba yiwuwar tura wata tawaga ta manyan jami’ai zuwa Najeriya, tare da haɗin gwiwa da abokan hulɗa na ƙasashen duniya domin ƙarfafa jajircewa wajen gudanar da sahihin zaɓe.

Source: Twitter
Frank ya ce jami’an zaɓe, jami’an shari’a da jami’an tsaro suna da muhimmiyar rawa wajen kare sahihancin zaɓe, don haka ya kamata a ƙarfafa su su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa.
Ya jaddada cewa ya kamata hukumomin tsaro su guji nuna goyon baya ga kowace jam’iyyar siyasa, tare da kare masu zaɓe ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke goyon baya ba.
Frank ya danganta sahihin zaɓe da shugabanci mai riƙon amana, bunƙasar tattalin arziki da zaman lafiyar ƙasa.
APC ta aika wasika ga INEC
Kun ji cewa jam’iyyar APC ta rubuta wa INEC wasiƙa, tana neman aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan amfani da rajistar mambobin jam’iyyun siyasa.
APC na magana ne kan miƙa rajistar mambobin jam’iyyun siyasa da kuma amfani da ita a zaɓen fidda gwani, tarukan jam’iyyu da manyan tarukansu.
Asali: Legit.ng
