Atiku vs Tinubu: Jam'iyyar ADC Ta Shata Layi, Ta Gindaya Sharadi kan Babban Zaben 2027

Atiku vs Tinubu: Jam'iyyar ADC Ta Shata Layi, Ta Gindaya Sharadi kan Babban Zaben 2027

  • Shugaban ADC na ƙasa, David Mark, ya ce jam’iyyar za ta bi ƙa’idojin zaɓe a 2027 amma ba za ta amince da duk wani yunƙurin yi mata magudi ba
  • Mark ya bayyana haka yayin da shugabannin Savannah Centre for Diplomacy, Democracy and Development suka ziyarci hedikwatar ADC ta ƙasa da ke Abuja
  • Tsohon Alkalin Alƙalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya buƙaci ADC ta tabbatar da cewa ’yan takararta da mambobinta sun bi dokokin INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, ya ce jam’iyyar za ta bi ƙa’idojin zaɓe a babban zaɓen 2027, amma ba za ta yarda da yunƙurin yi mata magudi ko hana ta nasara ba.

Mark ya bayyana hakan ne ranar Laraba lokacin da mambobin Kwamitin Gudanarwa na Savannah Centre for Diplomacy, Democracy and Development suka ziyarci hedikwatar jam'iyyar ADC ta ƙasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Yayin kokarin kifar da Tinubu, ADC ta yi gargadi kan magudi a 2027

David Mark.
Shugaban jam'iyyar adawa ta ADC na kasa, Sanata David Mark Hoto: David Mark
Source: Twitter

Premium Times ta ruwaito cewa tsohon Alkalin Alƙalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ne ya jagoranci tawagar, wanda shi ne shugaban Council of the Wise na cibiyar.

A cewar wata sanarwa daga ofishin Sakataren Yaɗa Labarai na ADC na ƙasa, ziyarar na daga cikin tattaunawar da cibiyar ke yi da jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki gabanin zaɓen.

Ariwoola ya nemi din doka

Ariwoola ya buƙaci shugabannin ADC su tabbatar da cewa ’yan takarar jam’iyyar da mambobinta sun bi ƙa’idojin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), tare da guje wa tashin hankalin siyasa.

Mark ya ce ADC ta himmatu wajen gudanar da harkokin siyasarta ta yadda za ta ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan tsarin dimokuraɗiyya.

“Mun himmatu wajen yin siyasa ta hanyar da za ta ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Ya ce jam’iyyar za ta bi ƙa’idojin INEC da kuma kundin ɗabi’ar cikin gida da ke kunshe a cikin littafin da aka fi sani da “Orange Book”, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku ya magantu kan tsadar kayan noma, ya fadi mafita tare da sukar Tinubu

ADC ta yi alkawarin bin doka

“Mun ɗora wa kanmu mafi girman ma’aunin kyakkyawar ɗabi’a a matsayin jam’iyyar siyasa. Za mu bi ƙa’idoji amma ba za mu yarda da magudi ba ko kuma mu bari a yi mana magudin da zai hana mu nasara,” in ji Mark.

Sabon jadawalin INEC ya tanadi gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu.

ADC .
Tambarin jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

An fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa ranar 19 ga Agusta, yayin da aka fara yaƙin neman zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi ranar 9 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027 ta fara daukar zafi, yan daba sun farmaki tawagar kamfen ADC

ADC ta ja hankalin INEC

Kun ji cewa ADC ta buƙaci INEC ta hana malaman jami’a da aka san suna da ra’ayin siyasa zama jami’an tattara da haɗa sakamakon zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce nada malaman jami’a da suka fito fili suka bayyana matsayinsu na siyasa na iya jefa sahihancin tsarin zaɓe cikin barazana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262