Lissafi Ya Canza wa APC da Kotu Ta Kuma Tsige ‘Dan Takaran Majalisar Dokoki

Lissafi Ya Canza wa APC da Kotu Ta Kuma Tsige ‘Dan Takaran Majalisar Dokoki

  • Ayuba Dalyop Mandung shi ne wanda zai yi wa mutanen kudancin Jos takara a zabe mai zuwa
  • Kotun tarayya a jihar Filato ta rusa takarar da Mancha John Vincent yake murna ya samu a APC
  • Dorcas Agishi ta bukaci APC ta daina yawo da sunan Mancha Vincent da sunan shi ne ‘dan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Plateau - Babbar kotun tarayya mai zama a garin Jos a jihar Filato ta ba Ayuba Dalyop Mandung nasara a shari’ar neman takara.

Alkali ya ce Ayuba Dalyop Mandung ya lashe zaben tsaida gwani na kujerar majalisa dokokin jiha mai wakiltar mazabar Jos a Filato.

Majalisar tarayya
Majalisar tarayya a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

APC: Kotu ta rusa takarar Ayuba Dalyop Mandung

Daily Trust ta rahoto cewa Dorcas Agishi ta hana APC amfani da sunan Mancha John Vincent a matsayin ‘dan takara a mazabar.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Dorcas Agishi ta yanke hukuncin ne sakamakon karar da Ayuba Mandung ya shigar kan APC, hukumar INEC da abokin gwabzawarsa.

Lauyan Ayuba Mandung ya yi ikirarin cewa an taba sakamakon zaben tsaida gwanin da APC ta shirya a ranar 20 ga Mayu 2026.

Lauya ya doke APC da INEC a kotu

Rahoton ya ce Ritji Timothy Yilwatda ya tsaya wa ‘dan siyasar kuma Mancha John Vincent ta gamsu da hujjojin da ya gabatar wa kotu.

Barista Ritji Timothy Yilwatda ya tabbatar wa kotu cewa an taba sakamakon zabe daga mazabar Giring bayan an fitar da sanarwa.

Alkali Dorcas Agishi ta ce ba a yi wa Mandung adalci ba domin jam'iyya ba ta saurare shi ba.

Mai shari’a ta yi hukunci cewa ba za a iya canza abin da aka rubuta kuma har aka sanar a matakin mazaba ba a cewar Premium Times.

Hukuncin ya tabbatar da nasarar wanda ya yi kara a matsayin ‘dan takaran Jos ta Kudu.

Kara karanta wannan

Bayan murabus a gwamnatin Tinubu, INEC ta saka sunan tsohon minista ya yi takara

Hukuncin da alkali ta yanke a Jos ta Kudu

Haka kuma an yi wa jam’iyyar APC umarni cewa Mancha Vincent ba shi ne halataccen ‘dan takara a zaben majalisar jihar ba.

Alkalin ta kuma bukaci wadanda ake kara su yi biyayya ga kundin tsarin mulki, dokokin APC da dokar zabe wajen bada tuta.

Abin bai tsaya nan ba, kotu ta wajabta gabatar wa INEC sunan Mandung a masayin ainhin ‘dan takaran Jos ta Kudu a badi.

Sannan an ci Vincent, jam’iyyar APC da kuma hukumar INEC tarar N500, 000 a wannan shari’a mai lamba FHC/J/CS/43/2026.

'Yan APC
Wasu magoya bayan jam'iyyar APC a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Instagram

An rusa zaben tsaida gwanin APC

Rahoton nan cewa ya yi bayan an fara kamfe sai aka ji alkali ta tsige wa jam’iyyar APC ‘dan takarar ‘dan majalisa a Jos.

Kotun tarayya ta ci jam’iyyar APC da ‘dan takaranta da kuma hukumar INEC tarar kudi da ta ce a sake shirya wani zaben.

A 2023 da kotu ta tsige Hon. Musa Bagos bayan samun kuri'u 95, 000 sai da hawan jini ya kashe wasu magoya bayansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng