An kama ma'aikacin gidan yari da wiwi

An kama ma'aikacin gidan yari da wiwi

- An cafke wani ma'aikacin gidan gyaran hali da wani ganye da ake zargin wiwi ce a Jos

- Wanda ake zargin mai suna Mista Uche Chikelu ya musanta zargin da ake masa

- Alkalin kotu ta bada umurnin a cigaba da rike wanda ake zargin hannun NDLEA zuwa ranar cigaba da sauraron kara

An kama ma'aikacin gidan yari da wiwi
Gudumar alkalin kotu. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Kyrgyzstan Jeenbekov ya yi murabus

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos ta tsare wani ma'aikacin gidan gyaran hali mai suna Danladi Bako bisa zargin mallakar wani abu da ake zargin tabar wiwi ce.

Mallakar tabar wiwi laifi ne da aka tanadarwa hukunci a sashe na 19 na dokar hukumar NDLEA.

Bayan an karanta laifin ga wanda ake tuhuma ya musunta zargin da ake masa.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

Sai dai lauyan wanda ake kara Uche Chikelu, ya roki kotun da ta dage sauraren karar don bashi damar gabatar da hujjoji da shaidu don kare kudirinsa, sannan ya yi kira da kotun da ta bar wanda ake zargin a gidan gyaran halin da ke Jos.

A nasa bangaren lauyan masu kara, B. I. Shehu ya roki kotun da ta damka shi ga hukumar NDLEA tunda dai shi daya ne daga cikin ma'aikatan gidan gyaran halin.

Da take yanke hukunci, mai shari'a Dorcas Agishi, ta yadda da kudurin lauyan wanda ake kara ta kuma dage shari'ar zuwa 19 ga watan Oktoba, 2020 don ci gaba da sauraren karar.

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya amince a ɗauki sabbin malamai 776 don inganta ilimi a makarantun gwamnatin jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne jim kadan bayan gana wa da ya yi da jami'an Ma'aikatar Ilimi na jihar a gidan gwamanti da ke Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164