Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus Ya Rungumi Kaddara bayan Rasa Tikitin Takara a Zaben 2027

Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus Ya Rungumi Kaddara bayan Rasa Tikitin Takara a Zaben 2027

  • Tsohon ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya janye shirin daukar matakin shari’a kan zaben fitar da dan takarar gwamna na APC a Oyo
  • Tsohon Ministan ya bukaci shugabannin APC su fara sulhu tsakanin ‘yan jam’iyyar gabanin babban zaben 2027
  • Ya ce akwai shaidu da takardun da ke nuna an samu kura-kurai da rashin adalci a tsarin zaben fidda gwani, amma ya hakura ya rungumi jaddara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Tsohon Ministan Wutar Lantarki, wanda ya nemi takarar gwamna a karkashin APC a Jihar Oyo, Adebayo Adelabu, ya janye daga shirin daukar matakin shari’a.

Adelabu ya bayyana cewa ya rungumi kaddara kan rashin nasararsa a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC a jihar Oyo, inda ya bukaci shugabannin APC su fara shirin sulhu.

Kara karanta wannan

Kofa ya ce APC za ta lashe Kano baki daya, Kwankwaso zai rasa kujeru a 2027

Adelabu.
Tsohon ministan wutar lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu Hoto: Adebayo Adelabu
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito vewa Adelabu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Ibadan, babban birnin jihar, inda ya ce matakin da ya dauka ba wai saboda rashin hujja ba ne.

Ya ce ya yanke shawarar hakan ne bayan wata ganawa da wasu shugabannin jam’iyyar da wakilan magoya bayansa daga kananan hukumomi 33 da mazabu 351 na jihar Oyo.

Me ya sa Adelabu ya janye shirinsa?

Adelabu ya ce a matsayinsa na mamba mai biyayya da jajircewa ga APC, ya yanke shawarar ba zai daukaka kara a cikin jam’iyyar ko kuma ya fara shari’a kan tsarin zaben fidda gwani a wannan lokaci ba.

Ya ce wannan mataki ba yana nufin ba shi da hujjoji ko kwarin gwiwa kan abin da yake ikirari ba.

Ya ce:

“Wannan shawara ba saboda rashin hujja, kwarin gwiwa ko yakini ba ce. Haka kuma bai kamata a fassara ta da cewa na mika wuya ba, ko kuma burina na zama gwamnan Jihar Oyo lamari ne da dole sai na cimma shi.”

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Adelabu ya ce an yi kura-kurai a APC

Ya ce ya zabi yin hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyyar, tare da kauce wa kara zurfafa rarrabuwar kawuna da rage hadin kan APC a jihar.

Adelabu ya kuma ce shugaban APC na kasa, a ziyarar da ya kai Oyo kwanan nan, ya amince cewa an samu kura-kurai, rashin adalci da wasu matsaloli a sassan tsarin zaben fidda gwani.

Ya ce ko da yake amincewa da kura-kurai ko neman afuwa abu ne mai muhimmanci, bai kamata hakan ya maye gurbin gyara matsalolin ba idan har akwai damar magance korafe-korafen da ake yi.

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @APCNigeria
Source: Twitter

Adelabu ya bukaci a yi sulhu a APC

Adelabu ya bukaci shugabannin APC na kasa su dauki matakan dawo da amincewa tsakanin ‘yan jam’iyyar, sake gina alaka da kuma tabbatar da hadin kai gabanin zaben 2027.

Ya ce burinsa shi ne a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyyar, tare da magance korafe-korafen da suka taso daga tsarin zaben fidda gwani, cewar rahoton Guardian.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu na da abubuwan da zai shawo kan 'yan Najeriya su zaɓi APC a 2027? An samu bayani

Masu neman takarar APC sun fusata

An ji cewa wasu daga cikin 'yan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Oyo da ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani ba.

Fusatattun masu neman takarar sun amince za su karɓi duk wata gayyata daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin warware rikicin da ya biyo bayan zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262