Seyi Tinubu Ya 'Kunyata' Bashir Ahmad a Wani Taron APC, an Yaɗa Bidiyon

Seyi Tinubu Ya 'Kunyata' Bashir Ahmad a Wani Taron APC, an Yaɗa Bidiyon

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi martani kan bidiyon da ke nuna Seyi Tinubu ya tsallake shi yayin gaisawa da mutane
  • Bashir Ahmad ya bayyana cewa sun raka Seyi Tinubu ne domin ganawa da kungiyar mata, ba wai domin ganawa da shi kai tsaye ba
  • Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda mutane da dama ke yi wa Bashir ba'a saboda yadda yake tallata APC da Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya yi magana kan bidiyon da ake yaɗawa a wani taron jam'iyyar APC da Seyi Tinubu.

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari ya fadi yadda za su tunkari talakawa su tallata Tinubu

An gano wani bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta da Seyi Tinubu ya ki gaisawa da shi lamarin ya jawo martani daga yan Najeriya.

Bashir Ahmad ya musanta cewa Seyi ya ki gaisawa da shi
Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: Twitter

Bidiyon Seyi: Bashr Ahmad ya yi magana

Bashir ya yi wannan martani ne a cikin sakon da wallafa a X inda ya ke bayyana gaskiyar abin da ya faru a yau Asabar 10 ga watan Oktobar shekarar 2026.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce ya kamata mutane su fahimci abin da ya faru kafin yada ƙarairayi.

Ya ce sun raka Seyi Tinubu ne domin ganawa da kungiyar mata da aka gani yana gaisawa da matan a bidiyon da ake yadawa.

Ya ce:

"Duk wannan hayaniyar da ake yi kan wani bidiyo alhali ba ku ma san ainihin abin da ya faru ba.
"Mun halarci taron tare da shi, ba mu je wurin ne domin ganawa da Seyi Tinubu ba, mun raka shi ne domin ganawa da ƙungiyar mata, waɗanda aka gan shi yana gaisawa da su tare da musabaha a cikin bidiyon."
An ga bidiyon da Seyi Tinubu ya ki gaisawa da Bashir Ahmad
Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da Bashir Ahmad. Hoto: Senator Seyi Tinubu, Bashir Ahmad.
Source: Facebook

Abin da Seyi Tinubu ya yi wa Bashir

Kara karanta wannan

'Sharri ne': Malami ya ce bai yi wa Tinubu, Shettima addu'a su yi nasara ba

An gano Seyi Tinubu yana gaisawa da mutane da dama a taron amma ya tsallake Bashir wanda ya jawo maganganu da.dama a ƙasar.

Seyi ya bi layi-layi inda yake gaisawa da mata da maza amma yana zuwa kan Bashir sai ya tsallake shi.

Bidiyon ya jawo martanin yan Najeriya da dama duba da yadda Bashir ya ke tallata gwamnatin APC da Bola Tinubu.

Mafi yawan mutanen suna yi masa ba'a da cewa tun yanzu ya kamata ya san matsayinsa a gwamnatin tarayya duba da irin rashin daraja shi da aka yi.

Bashir Ahmad ya magantu kan zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa Bashir Ahmad ya ce bai yarda da kallon kwamitin yakin neman zaben APC a 2027 a matsayin yaƙi tsakanin masu danniya da wadanda ake zalunta ba.

Bashir wanda jigo ne a tafiyar City Boys Movement ya ce ya kamata a tantance APC ne bisa manufofinta, shirye-shiryenta, tarihinta da ƙwarewar shugabanninta.

Ya bayyana haka ne a matsayin martani ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.