Jigo a APC, Adamu Muhammad, ya rasu

Jigo a APC, Adamu Muhammad, ya rasu

- Jigon jam'iyyar APC, Adamu Muhammad, ya rasu a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba

- Muhammad ya amsa kiran mahaliccinsa a asibitin Yola bayan ya yi fama da rashin lafiya

- Gwamna Fintiri da Nuhu Ribadu sun mika ta'aziyyarsu a kan mutuwar marigayin

Allah ya yi wa jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa, Alhaji Adamu Muhammad rasuwa.

Muhammadu ya rasu a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba, a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Yola, inda ya kwashi dan lokaci yana jinya.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya mika ta’aziyyarsa ga jam’iyyar APC a kan rasuwar jigon nata, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban sakataren labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba.

Jigo a APC, Adamu Muhammad, ya rasu
Jigo a APC, Adamu Muhammad, ya rasu Hoto: Fombina Times
Asali: UGC

Fintiri wanda ya bayyana mutuwar a matsayin na bazata, ya kuma mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, masarautar Mubi a kan rashi da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Ni ba matar yara ba ce, ta manya ce — Jaruma Rashida Maisa’a

Ya bayyana cewa za a dunga tunawa da Muhammad saboda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Adamawa.

Ya bukaci APC da ta dauki dangana da imani da Allah, inda ya bayyana marigayin a matsayin babban jigo ga jam’iyyar wanda ya yi amfani da kwarewarsa wajen ci gaban jam’iyyar da jihar baki daya.

Hakazalika, tsohon Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Malam Nuhu Ribadu ya mika nasa ta’aziyar ga APC kan rasuwar jigon nata.

Ribadu wanda ya bayyana kyawawan halayyar marigayin, ya ce Muhammad ya kasance mutum mai jama’a, salihi na akika, kuma mai halayya na kwarai, jaridar Fombina Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Ƴan majalisa suna shirin haramtawa kotu korar shugaban ƙasa da gwamnoni

Ya bayyana cewa marigayin ya kasance dan siyasa mai amana wanda baya taba zubar da mutuncinsa saboda son rai.

“Malam Adamu ya kasance dan siyasa mafi amana da na hadu da shi tun bayan shigana harkar siyasa," in ji shi

Ribadu ya yi wa marigayin addu’an samun rahmar Allah sannan ya roki Ubangiji ya ba iyalansa juriyar wannan rashi da suka yi.

A wani labarin, rikicin cikin jam'iyyar APC ta jihar Zamfara na cigaba da aukuwa tsakanin bangarorin guda biyu, wanda har kotu bata gama hukunci akai ba, Legit.ng ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel