Masoyan APC Sun Yi Hatsarin Mota a kan Hanyar zuwa Gangamin Tinubu, Shettima
- Wasu magoya bayan APC sun yi hatsarin mota a Lafia, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa babban gangamin Tinubu
- Hadarin ya faru ne a ranar Asabar bayan motar bas ɗin da ke ɗauke da magoya bayan ta yi karo da wata mota mai zuwa
- Daniel Ihomun ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce babu wanda ya mutu, amma an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Wasu magoya bayan jam’iyyar APC a Benue sun yi hatsarin mota yayin da suke tafiya zuwa Lafia.
Lamarin ya faru ne yayin da suke shirin zuwa Nasarawa, domin halartar babban gangamin yankin Arewa ta Tsakiya na nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu.

Source: UGC
Yan APC sun yi hatsarin mota a Benue
Wani ganau ya shaida wa Punch cewa motar bas ɗin da ke ɗauke da magoya bayan daga jihar Benue ta yi karo da wata mota da ke tafe daga gaba a cikin garin Lafia ranar Asabar.
Da aka tuntube shi, Daniel Ihomun, sakataren yaɗa labarai na ɓangaren APC a Benue ƙarƙashin jagorancin Austin Agada, wanda ke goyon bayan Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ihomun ya ce waɗanda hatsarin ya rutsa da su magoya bayan Akume ne, waɗanda suka tafi Lafia domin halartar gangamin.
Ya ce:
“Gaskiya ne wasu magoya bayan APC daga Benue, waɗanda ke biyayya ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, sun yi hatsarin mota a yau yayin da suke zuwa babban gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu.
“Hadarin ya faru ne a cikin garin Lafia. Godiya ga Allah, babu wanda ya mutu, amma an kai waɗanda hatsarin ya rutsa da su asibiti."
Yadda hatsarin motar da ya faru
Hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da magoya bayan APC daga sassa daban-daban na yankin Arewa ta Tsakiya suka taru a Lafia domin halartar gangamin da aka shirya don nuna goyon baya ga Tinubu da Shettima gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sanar da shirin gudanar da gangamin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, bayan wani babban taron shugabannin APC na yankin Arewa ta Tsakiya a Abuja.
An shirya taron ne ƙarƙashin kulawar ƙungiyar North-Central Grassroots Mobilisation Network, wadda ke ƙoƙarin tattara magoya baya daga matakin ƙasa domin nuna goyon baya ga jam’iyyar. Meta Description
Shettima ya roka wa Tinubu alfarma
Mun ji cewa Kashim Shettima ya ce tattalin arzikin Najeriya na dab da durƙushewa kafin cire tallafin fetur da daidaita farashin musayar kuɗi.
Ya roƙi ’yan Najeriya su yi haƙuri da Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa matakan da ya ɗauka sun taimaka wajen kare tattalin arzikin ƙasar.
Shettima ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar wahalhalu, amma ya ce gwamnati na shirya wasu shirye-shiryen rage musu matsin rayuwa.
Asali: Legit.ng

