Alkawarin da Aka Yi wa Dalibai Idan Atiku Ya Ci Zabe Bayan Kunci a Mulkin Tinubu
- Daraktan yaƙin neman zaɓen ADC na Atiku Abubakar, Sanata Austin Akobundu, ya ce Atiku zai duba bashin ɗalibai Akobundu ya ce Atiku zai rage tsadar rayuwa ta hanyar rage kuɗin sufuri, samar da wutar lantarki mai araha, inganta ilimi da kiwon lafiya
- Ya kuma yi alƙawarin ƙarfafa tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga matasa, tallafa wa manoma da tabbatar da ci gabansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Daraktan Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ADC da Atiku Abubakar, Sanata Austin Akobundu, ya yi magana kan shirin NELFUND.
Akobundu ya ce Atiku Abubakar zai sake duba tsarin Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND), ya nemi afuwar bashin ɗalibai tare da inganta damar samun ilimi.

Source: Facebook
Akobundu ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, lokacin bikin ƙaddamar da Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen ADC a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja, cewar Tribune.
ADC ta fara daukar alkawura ga yan Najeriya
Ya ƙara da cewa gwamnati ya kamata ta taimaka wa matasa su koyi sana’o’i da ƙwarewa ba tare da ƙara wa iyalansu nauyin kuɗi ba.
A cewarsa, ya karɓi naɗin cikin kan-kan da kai, tare da fahimtar nauyin da ke kansa. Ya bayyana aikin a matsayin kira na jagorantar kamfen ga ’yan Najeriya da ke fama da wahalar biyan buƙatun yau da kullum.
Ya ce:
“Wannan ba aikin biki ba ne. Aiki ne na jagorantar kamfen ga ’yan Najeriya da ke tambayar wata muhimmiyar tambaya: Ta yaya zan iya biyan kuɗin rayuwa? Ga iyayen da dole ne su zaɓi tsakanin biyan kuɗin makaranta da sayen abinci. Ga ma’aikacin da albashinsa ke ƙarewa wajen biyan kuɗin sufuri da haya."
Ya ce gwamnatin APC ta bukaci ’yan Najeriya su jure wahala kusan shekaru huɗu, amma iyalai ba za su iya rayuwa da alƙawura kawai ba.

Kara karanta wannan
Ya mutane za su samu fetur mai araha a garuruwan da babu gidan man NNPC? An aika sako ga Tinubu

Source: Getty Images
Bangaren da Atiku zai mayar da hankali
Akobundu ya ce kamfen ɗin zai mayar da hankali kan buƙatun yau da kullum na ’yan Najeriya, ciki har da samar da abinci mai araha, rage kuɗin sufuri, samar da ingantacciyar wutar lantarki.
Ya ce shirin tattalin arzikin Atiku zai fifita samar da kayayyaki da sauƙaƙa tsadar rayuwa, cewar Punch.
Ya ƙara da cewa Atiku Abubakar zai dawo da tallafin man fetur da aka tace a Najeriya, wanda za a tsara shi bisa kasafin kuɗi, tun daga ranar farko ta mulkinsa.
Akobundu ya ce rage kuɗin man fetur da sufuri zai kusantar da kasuwanni ga masu sayayya, ya sa abinci ya fi sauƙin samu, tare da bai wa ’yan kasuwa damar ƙara samar da kayayyaki da biyan ma’aikatansu.
Atiku ya sake caccakar Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Atiku Abubakar ya soki matakin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na bayar da rangwamen fetur na kwanaki 30, yana mai cewa ba zai magance matsin tattalin arziki ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin Tinubu ta kwaikwayi shawararsa ta tallafa wa fetur da aka tace a Najeriya, amma ba dari bisa dari ba.
Atiku ya kuma bukaci a tabbatar da gaskiya a zaben 2027, tare da yin kira ga jam’iyyarsa ta ADC da ta kai sakon yakin neman zabenta ga al’ummar Najeriya.
Asali: Legit.ng

