Abin da Muka Sani kan Alakar Sanata Yari da Yan Majalisa 8 da Suka Bar APC

Abin da Muka Sani kan Alakar Sanata Yari da Yan Majalisa 8 da Suka Bar APC

  • Jigo a APC, Sani Abdullahi Shinkafi, ya yi magana kan ’yan majalisar Zamfara takwas da suka fice daga jam’iyya mai mulki
  • Shinkafi ya bayyana cewa Abdulaziz Yari ya yi ƙoƙarin sasanta rikicin ’yan majalisar da shugabancin majalisa
  • Ya kuma musanta zargin cewa Yari ne ke ɗaukar nauyin ɗan takarar gwamnan ADC, Bilyaminu Yusuf Shinkafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Wani jigo a jam’iyyar APC, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya yi martani kan ficewar yan majalisar dokoki a Zamfara.

Shinkafi ya musanta ikirarin cewa danganta Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari da wasu ’yan majalisar dokokin jihar Zamfara takwas da aka dakatar, waɗanda suka yi murabus daga jam’iyya mai mulki a baya-bayan nan.

An wanke Sanata Yari kan zargin alaka da ADC
Sanata Abdulaziz Yari yana jawabi a taro. Hoto: Senator Abdulaziz Yari.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 10 ga Oktoba, 2026, Shinkafi ya ce ’yan majalisar ba su da kusanci a siyasance da Yari, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

2027: Arewa ta shirya gagarumin gangamin tallata Tinubu da Shettima

Kokarin Yari na yi sulhu da yan majalisar

Ya ce Yari da sauran masu ruwa da tsaki a APC sun yi ƙoƙarin samar da sulhu tsakanin ’yan majalisar da aka dakatar da shugabancin majalisar dokokin jihar.

Sai dai ƙoƙarin ya ci tura saboda shugabancin majalisar ya ƙi janye dakatarwar, tare da fara shari’ar laifi kan ’yan majalisar.

A cewar Shinkafi, an dakatar da ’yan majalisar a ranar 26 ga Fabrairu, 2024, bisa zargin aikata manyan laifukan da suka haɗa da rashin ɗa’a, haɗa baki, tayar da hankali.

Ya ce rikicin ya ci gaba duk da ƙoƙarin samar da mafita ta siyasa, lamarin da ya sa ’yan majalisar da abin ya shafa suka rasa albashi, alawus da sauran haƙƙoƙinsu.

Ya ƙara da cewa ’yan majalisar sun shigar da ƙorafi ga Kwamitin Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai ta Tarayya, domin ya shiga tsakani tare da shawo kan majalisar dokokin jihar da gwamnati su mayar da su bakin aikinsu kuma su biya haƙƙoƙin da suka tara.

Kara karanta wannan

Majalisar koli ta addinin Musulunci ta sake magana kan zargin kisan Kiristoci

Shinkafi ya yi iƙirarin cewa tarihin siyasar ’yan majalisar ya nuna cewa ba su kafa wata ƙungiya ta siyasa da ke biyayya ga Yari ba, cewar Punch.

Ya ce biyar daga cikin ’yan majalisar takwas sun lashe zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a babban zaɓen 2023, kafin daga bisani su sauya sheƙa zuwa APC.

Shinkafi ya wanke Sanata Yari kan zarge-zargen da ake yi masa
Jigon APC a jihar Zamfara, Sani Abdullahi Shinkafa. Hoto: Sani Abdullahi Shinkafi.
Source: Facebook

Zargin Yari da alaka da dan ADC

Shinkafi ya kuma yi watsi da zarge-zargen da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Yari ne ke ɗaukar nauyin ɗan takarar gwamnan Zamfara na jam’iyyar ADC, Hon. Bilyaminu Yusuf Shinkafi.

Ya bayyana zarge-zargen a matsayin ƙarya da kuma ƙoƙarin ɓata suna, yana mai cewa abokan hamayyar siyasar Yari ne suka shirya yaƙin ɓatanci.

A cewarsa, ɗan takarar ADC ɗin yana da alaƙar yan uwantaka da Yari, amma tsohon gwamnan ba ya ɗaukar nauyin siyasarsa, cewar Punch.

Yadda APC za ta tallata Tinubu

Mun ba kawo muku rahoton cewa Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana shirye-shiryen da suke domin tunkarar zaben shugaban kasa na 2027 karkashin jam'iyyar APC.

Ya bayyana haka ne a wata hira bayan bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai kaddamar da kamfen din shi a jihar Kaduna.

Sanata Yari ya sanar da cewa jam'iyyar APC da Bola Tinubu ba su tsoron Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben da suka tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.