'Ya'yan talakawa da muke wulakantawa za su iya zama ajalin mu - Shettima

'Ya'yan talakawa da muke wulakantawa za su iya zama ajalin mu - Shettima

- Sanata Kashim Shettima ya janyo hankalin takwarorinsa kan halin ko in kula da gwamnatoci ke yi kan makarantun gwamnati

- Tsohon gwamnan na jihar Borno ya koka kan yadda gwamnati ba ta mayar da hankali kan bawa 'ya'yan talakawa ilimi

- Dan majalisar na tarayya ya ce yaran talakawa za su zama fitina a kasar muddin ba a basu ingantaccen ilimi ba

Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ya janyo hankalin gwamnati kan tabarbarewar ilimi da makarantu a jihohin Najeriya inda ya ce hakan zai zama fitina ga kasar a nan gaba idan ba a dauki mataki ba.

A wata faifan bidiyo da ke yawo a kafar Twitter, Shettima ya koka kan halin ko in kula da gwamnatoci ke nuna wa kan batun inganta ilimi a makarantun gwamnati.

Gwamnan ya bayar da misali da kasar India inda ya ce ana amfani da fasahar zamani wurin koyar da dalibai masu yawa inda ya yi kiran a fara amfani da irin wannan tsarin a Najeriya.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

Wani bangare cikin abinda ya fadi a bidiyon "Tabbas tarihi ba zai manta da rawar da muka taka ba idan muka bari makarantun gwamnati suka lalace a kasar nan.

"Muna kai yaran mu makarantun kudi amma kuma idan lokacin zabe ya zo sai mu yi amfani da yaran talakawa a matsayin 'yan bangar siyasa. Ku sani cewa yaran talakawar da mu kayi watsi da su za su iya rikidewa su zama fitar da za ta halaka dukkan mu."

Dan majalisar ya nuna takaicinsa kan yadda kasashen duniya ke cigaba yayin da Najeriya har yanzu tana fama da rikicin makiyaya da manoma da sauran wasu matsalolin da sauran kasashen duniya sun dade da warware su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel