Bayan Rasuwar Mai Martaba Alhaji Bello, Gwamma Lawal Ya Nada Sabon Sarkin Zurmi
- Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince da nadin Alhaji Aminu Atiku a matsayin sabon Sarkin Zamfaran Zurmi
- Aminu Atiku ya zama Sarkin Zamfaran Zurmi na 21 bayan rasuwar magabacinsa, Alhaji Bello Suleiman
- Gwamna Lawal ya bukaci sabon Sarkin ya tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a masarautar Zurmi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gusau, Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da nadin Alhaji Aminu Atiku a matsayin sabon Sarkin Zamfaran Zurmi.
An sanar da nadin sabon Sarkin ne ranar Litinin ta cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Abubakar Mohammad Nakwada, ya fitar.

Source: Facebook
Sakataren yada labarai da hulda da jama'a na Nakwada, Suleiman S/Tudu, ne ya fitar da sanarwar a Gusau, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Yadda aka zabi sabon Sarkin
Sanarwar ta bayyana cewa nadin ya biyo bayan tuntuba da kuma shawarar masu zaben Sarki na majalisar masarautar Zurmi.
An ce an gudanar da tsarin ne bisa al'adu da ka'idojin masarautar da kuma dokokin da suka dace na jihar Zamfara.
Kafin nadinsa a matsayin Sarki, Alhaji Aminu Atiku yana rike da sarautar Dangaladiman Zurmi.
Yanzu ya zama Sarkin Zamfaran Zurmi na 21, inda ya gaji marigayi Alhaji Bello Suleiman, wanda ya rasu ranar 31 ga watan Agusta, 2026.
Tarihin sabon Sarkin Zurmi
Sabon Sarkin shi ne babban dan marigayi Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya kasance Sarkin Zurmi na 19.
A baya kuma, Aminu Atiku ya taba zama shugaban riko na karamar hukumar Zurmi.
Da yake taya sabon Sarkin murna, Gwamna Dauda Lawal ya bukace shi da ya gina kan kyawawan abubuwan da magabatansa suka bari.
Gwamnan ya ce sabon Sarkin ya kamata ya mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya, adalci, hadin kai da kuma jin dadin jama'a.
Gwamna Lawal ya ba Sarkin umarni
Gwamna Lawal ya bayyana masarautar Zurmi, wadda dangin Alibawa suka kafa tun shekaru aru-aru da suka gabata, a matsayin muhimmiyar cibiya a tarihin jihar Zamfara.
Ya ce masarautar tana da dadadden tarihi da ya ginu kan ilimi, adalci da hidima ga jama'a.
Gwamnan ya kuma bukaci sabon Sarkin ya karfafa hadin kai da zaman lafiya tsakanin al'ummomin da ke karkashin masarautarsa.

Source: Facebook
Haka kuma ya bukace shi da ya inganta hadin gwiwa tsakanin masarautar, gwamnatin jihar da hukumomin tsaro domin kara tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Gwamna Lawal ya tabbatar wa sabon Sarkin da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar, yana mai cewa yana da yakinin mulkinsa zai taimaka wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban masarautar Zurmi da jihar Zamfara baki daya.
An nada sabon Sarkin Gumel
Kun ji cewa Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17.
Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani zai gaji mahaifinsa, Mai Martaba Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, wanda ya rasu ranar Alhamis, 3 ga Satumba 2026.
Marigayin ya rasu bayan ya shafe shekaru 46 yana mulkin masarautar Gumel, inda ya yi mulki mai cike da daraja da hidima ga al’ummarsa.
Asali: Legit.ng

