Da Wace Doka Alkali Ya Dogara Wurin Rushe Takarar Atiku da Shugabancin ADC?

Da Wace Doka Alkali Ya Dogara Wurin Rushe Takarar Atiku da Shugabancin ADC?

  • Mai shari’a Peter Lifu ya ce takardar murabus ɗin Nafiu Bala Gombe da tawagar David Mark ta gabatar ba ta da sahihanci
  • Alkalin ya bayyana cewa ikon NEC na gudanar da harkokin ADC ba zai ba ta damar kauce wa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya ba
  • Kotu ta soke shugabancin David Mark, ta kuma amince da Nafiu Gombe a matsayin zaɓaɓɓen ɗan kwamitin gudanarwar ADC da wa’adinsa bai ƙare ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Rikicin shugabancin jam’iyyar ADC ya ɗauki sabon salo bayan Mai shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya soke shugabancin Sanata David Mark da sauran jami’an da suka karɓi ragamar jam’iyyar a watan Yulin 2025.

Sai dai hukuncin da kotun ta yanke ranar 5 ga watan Nuwamban 2026 bai tsaya kan takaddamar shugabancin jam’iyyar kawai ba.

Kara karanta wannan

Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027

An rusa takarar Atiku
Shugaban ADC, David Mark, Nafiu Bala da Atiku Abubakar. Hoto: ADC Vanguard, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

A cikin kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da sahihancinsa (CTC), wanda jaridar Saturday Vanguard ta samu, Mai shari’a Lifu ya bayyana wasu manyan kurakurai a hujjojin waɗanda ake ƙara.

Kura-kuran sun haɗa da takardar murabus ɗin da ake takaddama a kanta, iyakokin ikon gudanarwa na NEC da kuma rashin gamsassun hujjojin da ke nuna cewa an zaɓi sabbin shugabannin ta hanyar dimokuraɗiyya.

Takardar murabus ɗin Nafiu Gombe

Ɗaya daga cikin manyan hujjojin tawagar David Mark ita ce cewa Nafiu Bala Gombe ya yi murabus da kansa daga muƙamin mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa a ranar 17 ga watan Mayun 2025, kafin taron NEC da ya samar da sabon shugabanci.

Tawagar Mark ta gabatar da takardar murabus ɗin a matsayin shaida mai lamba ADC 1, domin tabbatar da cewa Gombe ya ajiye muƙaminsa kuma saboda haka ba shi da hurumin ƙalubalantar sauyin shugabancin da ya biyo baya.

Maimakon ya amince da takardar kawai saboda an tabbatar da sahihancin kwafinta, alkalin ya kwatanta sa hannun da ke cikinta da sauran sa hannun Nafiu Bala Gombe a wasu takardu da aka sanya a gaban Kwamishinan Rantsuwa.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027

Ya bayyana cewa tabbatar da sahihancin kwafin takarda ba yana nufin an tabbatar da sahihancin sa hannun da ke cikinta ba, musamman idan ana takaddama a kansa.

Bayan kwatanta takardun, alkalin ya ce ya gano manyan bambance-bambance a tsarin rubutun sa hannun, salon yadda aka yi shi da kuma yadda aka sanya shi a takardun.

Saboda haka, ya bayyana takardar murabus ɗin a matsayin wadda aka ƙirƙira ko aka yi ta da manufar yaudara, tare da ƙin amincewa da ita a matsayin sahihiyar hujjar cewa Gombe ya yi murabus da kansa.

Rashin hujjar zaɓen sababbin shugabanni

A cewar alkalin, babban raunin da ke cikin hujjojin waɗanda ake ƙara shi ne rashin gamsassun bayanai da ke nuna cewa an zaɓi sabbin shugabannin ta hanyar dimokuraɗiyya.

Waɗanda ake ƙara sun dogara da wasu takardu da ke nuna cewa INEC ta samu sanarwar gudanar da taron NEC, ta sa ido kan yadda aka gudanar da taron sannan daga baya ta amince da shugabancin da aka samar.

Sai dai Mai shari’a Lifu ya bambanta tsakanin sanar da INEC gudanar da taro da kuma gudanar da sahihin zaɓen shugabanni, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yadda hukuncin kotu ya sake kara damuwar da Atiku da jam'iyyar ADC ke ciki

Ya bayyana cewa kasancewar jami’an INEC a taron ba ta tabbatar da cewa an bai wa mambobin jam’iyyar ko wakilan da aka zaɓa damar shiga taron da kuma kaɗa ƙuri’a ga waɗanda suke so ba.

Sai dai alkalin ya yi watsi da hujjar

Ya dogara da hukuncin Kotun Ƙoli a shari’ar Peoples Democratic Party v. Sule Lamido & Ors., inda ya bayyana cewa duk da cewa ya kamata kotuna su guji tsoma baki cikin zaɓin siyasa na cikin gida, ba za su iya ƙin sa baki ba idan ana zargin jam’iyya da karya tanade-tanaden kundin tsarin mulki ko wata doka.

Ya kuma yi watsi da hujjar cewa Nafiu Gombe ya kamata ya fara amfani da hanyoyin warware rikici na cikin gida kafin ya kai ƙara kotu.

Alkalin ya ce wannan ƙalubale bai da isasshen ƙarfi a wannan yanayi, saboda rikicin ya shafi bin dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma sauran dokokin ƙasa.

Hukuncin ƙarshe da alkalin ya yanke

Bayan nazarin dukkan muhimman batutuwan da ke cikin ƙarar, Mai shari’a Lifu ya soke shugabancin David Mark da sauran jami’an da ake takaddama a kansu.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: "Hukuncin kotu bai rusa takarar Atiku a 2027 ba"

Ya kuma soke dukkan ƙudurorin da aka cimma a taron NEC na ADC karo na 99 da aka gudanar a ranar 29 ga watan Yulin 2025.

Haka kuma, ya hana shugabannin da hukuncin ya shafa ci gaba da bayyana kansu a matsayin jami’an jam’iyyar ADC.

Alkalin ya kuma bayyana Nafiu Gombe a matsayin mamba ɗaya tilo da aka zaɓa a cikin kwamitin gudanarwar NWC wanda wa’adin mulkinsa na shekaru huɗu bai ƙare ba, kuma yake da hurumin kula da harkokin jam’iyyar bisa doka.

Atiku zai yi takara - ADC

An ji cewa ADC ta tabbatar da cewa za ta shiga zaɓen 2027 duk da rikicin shugabanci da ƙalubalen shari’a da take fuskanta.

Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai kasance cikin ’yan takarar 2027.

Ya zargi APCda amfani da rikicin shari’a wajen raunana jam’iyyun adawa domin Shugaba Bola Tinubu ya fuskanci ƙarancin hamayya a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.