Yan Bindiga Sun Afkawa Masallata a Sallar Asuba a Zamfara, an Rasa Rai yayin Harin
- Yan bindiga sun kai hari kan masallaci yayin sallar Asuba a garin Kaura, da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara
- Maharan sun kashe wani mutum mai suna Nasiru Sani Kaura tare da yin awon gaba da wasu masu ibada da dama
- Harin ya sake jefa al'ummar yankin cikin fargaba, yayin da mazauna garin ke fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara – ’Yan bindiga sun kai wani mummunan hari kan masu ibada a wani masallaci lokacin sallar asuba.
Majiyoyi suka ce lamarin ya faru ne a yankin Low Cost, a garin Kaura, karamar hukumar Kaura-Namoda ta jihar Zamfara.

Source: Twitter
Yadda maharan suka kai hari a masallaci
Wakilin Legit Hausa ya samu wannan rahoton ne daga shafin Bakatsine da ke kawo labarun tsaro musamman a yankin Arewacin Najeriya.
Maharan sun kai farmakin ne da safiyar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, 2026, lokacin da al'ummar Musulmi ke gudanar da sallar Asuba.
Rahoton da aka samu ya nuna cewa maharan sun kashe mutum guda mai suna Nasiru Sani Kaura tare da yin garkuwa da wasu masu ibada da dama.
’Yan bindiga sun farmaki masu ibada a Zamfara
Harin ya faru ne a wani lokaci da ya kamata jama'a su kasance cikin kwanciyar hankali domin gudanar da ibadarsu.
Lamarin ya kara jaddada matsalar rashin tsaro da al'ummar karamar hukumar Kaura-Namoda ke fuskanta, musamman hare-haren ’yan bindiga da sace mutane.
Mazauna yankin na bukatar karin tsaro
Harin ya tayar da hankalin al'ummar yankin, musamman ganin yadda maharan suka kai farmaki har cikin masallaci yayin da jama'a ke gudanar da ibada.
Mazauna yankin na bukatar daukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu tare da dakile sake afkuwar irin wadannan hare-hare.
Ƙarin bayani na tafe.....
Yan bindiga sun kashe limami a Sokoto
Mun ba ku labarin cewa 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani mummunan harin ta'addanci a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.
Hatsabiban sun hallaka limami da wasu mutane uku tare da yin garkuwa da wasu daban zuwa cikin daji a yayin harin.
Mutanen yankin sun koka da cewa harin ya jefa su cikin tsaro da fargaba inda da dama daga cikinsu suke shirin daina kwana a garin.
Asali: Legit.ng

