Pantami Ya Shirya Tona Asirin Wadanda Suka Kulla Masa Munafurci kan Takara

Pantami Ya Shirya Tona Asirin Wadanda Suka Kulla Masa Munafurci kan Takara

  • Farfesa Isa Ali Pantami, ɗan takarar gwamnan Gombe a PDP, ya gode wa magoya bayansa bisa addu’o’i da goyon bayan da suke nuna masa
  • Pantami ya bukaci magoya bayansa da kada su karaya saboda izgili da ake yi musu kan addu’o’in neman nasarar tafiyar siyasar Pantamiyya
  • Tsohon ministan ya yi zargin cewa an kashe makudan kudade domin kawo cikas ga tafiyarsa, yana mai cewa nan gaba zai tona asirin makircin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Professor Isa Ali Pantami, ya yi godiya ga masoyansa.

Pantami ya yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da harkokinsu na siyasa ba tare da tsoro ko shakku ba.

Pantami ya godewa masoyansa duk da kalubalen da suka shiga
Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Farfesa Pantami ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar.

Kara karanta wannan

Siyasa na ɗaukar zafi, ƴan daba sun farmaki ɗan takarar majalisa, an rasa rai

Pantami ya yi godiya ga masoyansa

Pantami ya bayyana cewa yana sane da mutanen da suke yi wa masu goyon bayan tafiyar Pantamiyya izgili, musamman waɗanda suke gudanar da addu’o’i a masallatai da coci-coci, tare da yin salloli da karatun Alƙur’ani domin neman nasarar jam’iyyar PDP.

Ya ce:

"Gombawa diban fari, ba a kwana da ku ba an tashi da ku, ina farawa da godiya ga yan uwa yadda ake mana addu'o'i da salloli a masallatai da coci-coci.
"Wallahi wannan yana kara mana karfin guiwa da jin dadi cewa Allah ya sa mutanenmu suna kaunarmu, ina addu'ar Allah ya fisshemu kunyan juna.
"Ina yabo da mutuntawa ga yan uwa yadda na ga duk da halin jarabawa da aka shiga amma ba su gajiya ba, sun tsaya tsayin daka suna neman jama'a ba gajiya wa."
Pantami ya shirya tona asirin munafukai a kan takararsa
Dan takarar gwamnan PDP a Gombe, Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Shawarar Pantami ga magoya bayansa

Farfesa ya shawarci magoya bayansa da kada su bari irin wannan izgili ya sanyaya musu gwiwa ko ya sa su yi kasa a guiwa, yana mai cewa har annabawa da sahabbai sun fuskanci irin waɗannan abubuwa a lokacin rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Bayan zargin son Pantami, Wike ya magantu kan taimakon wani dan takara

Pantami ya kuma jaddada cewa bai kamata a yi wa mutanen da suke neman taimakon Allah izgili ba, domin hakan na nuna rashin fahimtar girman Allah da kuma muhimmancin dogaro gare shi.

Ya kara da cewa:

"Ina ganin wasu na yi muku izgili a kan kuna yin addu'a, wanda kake rokon Allah amma yana maka izgili tabbas bai san Allah ba, kuma ba makiyinka ba ne tausayinsa ya kamata ka yi.
"Jama'ar da kuke zargi da kunna wuta daga lokaci zuwa lokaci wallahi zarginku gaskiya ne, dukkan bincike ya tabbatar da cewa babu kudin da ba a kashe ba domin a tabbatar da an cutar da wannan tafiya, amma abin da muka sani wannan tafiyar ta Allah ce.
"Nan gaba kadan za mu wayar muku da kai da isassun bayanai kan munafurcin da aka kulla da kuma wadanda suka kulla."

Wike ya yi magana kan takarar Pantami

A baya, an ji cewa Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa bai taba haduwa da tsohon ministan sadarwa kuma dan takarar PDP a jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami ba.

Ministan Abuja ya bayyana cewa gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya na zarginsa da goyon bayan takarar gwamna da Pantami ke yi a PDP.

Wannan na zuwa ne yayin da Wike ke .usayar yawu da wasu daga cikin gwamnonin APC, wadanda ba su goyon bayan gamayyar da ya kirkiro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.