Jerin lokutan da Buhari ya tafi jinya Ingila tsakanin 2015 da yanzu
Tun lokacin da ya hau mulki a 29 ga Mayun 2015, shugaba Buhari ya tafi jinya wata biyar,kuma ya kwashe kwanaki 170 cikin kwanaki 1,987 na mulkinsa a Landan.
Legit ta kawo muku cewa, a ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.
A cewar majalisar, yin hakan zai tabbatar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ya koma hayyacinsa a cikin shekarar nan.
Kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito da alaka a tsakanin bangarorin gwamnati ne ya yi wannan gargadi yayin da babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansa domin kare kasafi kudin shekarar 2021.
Karanta cikakken labarin a nan
KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 264
Jaridar Vanguard ta tattaro lokutan da shugaban kasa ya tafi jinya kasar waje.
Ga jerin nan mun kaow muku:
- Febrairu 5-10, 2016: Buhari ya dau hutun kwanaki shida zuwa Birtaniya inda yayi ikirarin cewa Likitocinsa na zaune a Ingila.
- 6-19 ga Yuni, 2016: Buhari ya tafi jinyar ciwon kunne Ingila inda ya kwashe kwanaki 13.
- 19 ga Junairu, 2017: Buhari ya kara zuwa Landan hutun jinya
- 5 ga Febrairu, 2017: Buhari ya aika wasika majalisar dokoki inda ya bukaci tsawaita kwanakin zamansa a Landan
Sai ranar 10 ga Maris, 2017 shugaban kasan ya dawo Najeriya amma bai koma bakin aiki ba. Hadimansa
- 7 ga Mayu, 2017: Buhari ya sake komawa Landan jinya. Bai dawo ba sai da ya kwashe kwanaki 104.
- 19 ga Agusta, 2017: Buhari ya dawo Najeriya, amma bai koma ofis ba saboda beraye sun bata ofishinsa, cewar fadar shugaban kasa.
- 8 ga Mayu, 2018: Buhari ya sake zuwa Landan duba lafiya
KU KARANTA: EndSARS: Akwai bukatar Sarakuna su ba gwamnati goyon-baya inji Buhari
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng