Kotu Ta Amince da Bukatar Matashin da Ake Zargi da Taba Mutuncin Gwamna a Facebook
- Kotu ta bada belin Fonya Sule, wanda aka tsare kan wani saƙon Facebook da ya shafi Gwamna Agbu Kefas da abokiyar takararsa, Zainab Ibrahim
- Gwamnatin Jihar Taraba ta shigar da ƙara tana zargin cewa saƙon ya ɓata sunan gwamnan da Zainab, wadda aka fi sani da Aunty Zee
- Lauyan Sule ya ce ana ɗaukar wanda ake zargi a matsayin marar laifi har sai kotu mai hurumi ta tabbatar da laifinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba, Nigeria - Wata babbar kotun tarayya da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, ta bayar da belin Fonya Sule, wanda aka tsare kusan wata guda a gidan yari.
An tsare matashin ne bisa zargin wallafa wani saƙo a Facebook da ya shafi Gwamna Agbu Kefas da ’yar takarar mataimakiyar gwamna ta jam’iyyar APC, Zainab Ibrahim.

Kara karanta wannan
Ana zargin yana tare da APC, Kwankwaso ya bada shawara kan sake zaɓen Tinubu a 2027

Source: Twitter
Premium Times ta ruwaito cewa an tsare Sule a gidan gyaran hali na Jalingo ne bayan gwamnatin Jihar Taraba ta shigar da ƙara kan saƙon, wanda ake zargin ya ɓata sunan gwamnan da Zainab, wadda aka fi sani da Aunty Zee.
Gwamnatin jihar, ta hannun ofishin babban lauyan gwamnati, ta shigar da ƙarar ne a ranar 30 ga Satumba a gaban babbar kotu da ke Jalingo.
Rubutun da Sule ya wallafa a Facebook
Takardun kotun sun nuna cewa Sule ya wallafa saƙon a shafinsa na Facebook a ranar 12 ga Agusta, 2026.
Saƙon ya ce:
"Aunty Zee ki kula sosai fa, idan ba haka ba da sannu za ki ɗauki ciki, maigidan naki kuwa mutum ne mai zuwa ɗaya.”
Zainab Ibrahim ita ce ’yar takarar mataimakiyar gwamna ta APC a Jihar Taraba a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnatin Taraba ta yi zargin cewa an wallafa saƙon ne da nufin ɓata sunan gwamnan da Zainab, inda ta bayyana lamarin a matsayin ɓata suna da kuma yaɗa bayanan ƙarya masu cutarwa.

Kara karanta wannan
Abin bakin ciki: Matashi ya kashe abokinsa da suke aiki wuri 1 kan gardamar siyasa
Neman belin wanda ake zargi
Lauyan Sule, Pius Danba, ya garzaya gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo domin neman a bayar da belin wanda yake karewa.
Ya bayar da hujjar cewa laifin da ake zargin Sule da aikatawa yana cikin waɗanda ake iya bayar da beli a kansu, sannan masu gabatar da ƙara ba su tabbatar da zarge-zargen da ake yi masa ba.

Source: Getty Images
Danba ne ya bayyana cewa kotun ta amince da buƙatar belin, yayin da yake magana da manema labarai a gidan gyaran halin Jalingo.
Ya zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan sharuddan belin ko ranar da za a ci gaba da sauraron shari’ar.
An kama mutum 2 kan rubutu a Facebook
Kun ji cewa jami'an yan sandan Kano sun kama mutum biyu mabiya Kwankwasiyya bisa taba kimar shugaban karamar hukumar Tofa, Yakubu Ibrahim Addis.
Wadanda yan sandan suka kama sun yi wani rubutu a shafin sada zumunta na Facebook, ana zargin sun soki ciyman kan aikin titin Lambu.
Asali: Legit.ng