Tabarbarewar Matsalar Tsaro Ta Kare a Najeriya, Inji Gwamnatin Buhari

Tabarbarewar Matsalar Tsaro Ta Kare a Najeriya, Inji Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin shugaba Buhari tace Sojoji da sauran hukumomin tsaro na samun nasara a kokarin dawo da zaman lafiya a Najeriya
  • Ministan labarai, Lai Muhammed, ya ce duk da akwai sauran yaƙi amma za'a iya cewa an magance mafi munin matsalar
  • A wurin taron haɗin guiwar ministoci hudu, Muhammed yace yan ta'adda sun rasa matsuguni kuma dakaru ba zasu sassauta musu ba

Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tace ta magance mafi munin matsalar tsaro a ƙasar nan. Ta ce yan ta'adda na kokarin guduwa amma ba zasu tsira ba.

The Nation ta ruwaito gwamnatin tarayya na cewa 'yan ta'adda, yan fashin daji da duk wasu gungun yan tada kayar baya basu da mafaka a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sheikh Pantami Ya Yi Nasara, FG Ta Dakatar Shirin Kara Kuɗin Kiran Waya da Data

Ta ƙara da cewa 'yan Najeriya ka iya ganin 'yan tsirarun Kes ɗin matsalar tsaro nan da can amma ba zai yi muni kamar yadda ta faru a baya ba.

Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed.
Tabarbarewar Matsalar Tsaro Ta Kare a Najeriya, Inji Gwamnatin Buhari Hoto: Lai Muhammed
Asali: UGC

An bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na Ministoci huɗu tare da babban Hafsan tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministocin sun haɗa da Alhaji Lai Muhammed (Yaɗa labarai), Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya (Tsaro), Rauf Aregbesola (Cikin gida) da Mohammed Maigari Dingyadi (Harkokin yan sanda).

Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed yace:

"Kamar yadda kowa ya sani, batun tsaro ya zama abinda muka fi tattauna wa a kai a baya-bayan nan, yan ta'adda, yan fashi da masu garkuwa a arewa maso Gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya."
"Rikicin yan aware da ɓarayin mai a kudu-kudu da kudu-gabas, sai kuma yan asiri, fashi da makami a kudu maso yamma. Yau mun zo mu faɗa muku, duk da bamu kai gaci ba, Sojoji da sauran jami'ai na samun nasarar dawo da zaman lafiya a hankali."

Kara karanta wannan

Bindigu Sama da Miliyan Shida Ke Yawo Hannun 'Yan Najeriya, Rahoto Ya Fallasa Wasu Bayanai

"A iya wahalar da muka fuskanta game da tsaro, zamu iya cewa an magance mafi munin ƙalubalen. Yan ta'adda, 'yan bindiga da sauransu ba zasu iya iko da wani sashi ba nan gaba a ƙasar nan."

Akwai sauran yaƙi - Lai Muhammed

Ministan ya ƙara da cewa Sojoji da sauran dakarun hukumomin tsaro sun ci nasara kuma suna kan samun nasara a yaƙin da suke da ayyukan ta'addanci sassan Najeriya.

"Saboda haka ba muna nufin yaƙi ya ƙare ba, abinda muke kokarin cewa shi ne Sojojin mu da jami'an sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar ɗauke mafi munin ƙalubalen da muke fama, kuma hakan na nufin mafi munin ya ƙare."
"A halin yanzu mun tasa yan ta'adda, yan fashin daji da sauran masu taimaka musu a gaba, kuma ba zamu sassauta musu ba har sai mun ƙarar da su baki ɗaya."

A wani labarin kuma Wani Rahoto Ya Bankado Yawan Miliyoyin Bindigun Dake Hannun Farararen Hula ba bisa doka ba a Najeriya

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

Wani Rahoto da aka bayyana ya nuna cewa akwai bindigu sama da miliyan Shida a hannun 'yan Najeriya.

Wannan na zuwa ne duk da namijin kokarin da gwamnati tace tana yi na dakile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel