Gwamnonin Arewa 5 da suka ce lallai mulki ya koma kudu a 2023

Gwamnonin Arewa 5 da suka ce lallai mulki ya koma kudu a 2023

Duk da cewa da sauran shekaru biyu a yi zaben 2023, an fara muhawara kan yankin da mulki zai koma bayan karewar wa'adin shugaba Muhammadu Buhari.

Har yanzu, manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya All Peoples Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) basu bayyana yankin da zasu baiwa tikitinsu ba.

Amma ana hasashen cewa tun da dan Arewa ke mulki yanzu, ya kamata mulki ya koma kudu a 2023.

Wasu gwamnonin Arewa biyar sun bayyana cewa wajibi ne mulki ya koma kudancin Najeriya a 2023.

Sun hada da:

1. Babagana Zulum (Borno)

A bikin murnar ranar haihuwan tsohon dan takaran gwamnan Rivers, Dakuku Peterside, Zulum yace: "Tsarin kama-kama alkawari ne mukayi, saboda hakan akwai bukatar mulki ya koma kudu."

2. Nasir El-Rufai (Kaduna)

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce mulki ya koma kudu a 2021.

Yace: "Daga Kudu ya kamata shugaban kasa ya fito a 2023; ban goyon bayan dan Arewa ya zama shugaba bayan Shugaba Muhammadu Buhari saboda yarjejeniyar siyasar Najeriya."

KU KARANTA: An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar

Gwamnonin Arewa 5 da suka ce lallai mulki ya zoma kudu a 2023
Gwamnonin Arewa 5 da suka ce lallai mulki ya zoma kudu a 2023
Asali: Twitter

KU KARANTA: An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar

3. Abdullahi Umar Ganduje (Kano)

Hakazalika, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce duk da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi tsarin kama-kama ba, akwai bukatar a yi amfani da shi don samun nasara a zabe.

4. Aminu Bello Masari (Katsina)

Gwamna Aminu Masari na Kastina ya yi kira ga kama-kama a 2023.

A cewarsa, don adalci da nuna daidaito, ya kamata a baiwa kudu damar mulkan Najeriya a 2023.

5. Abdullahi Sule (Nasarawa)

Kwanakin baya, gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna goyon bayansa ga tsarin kama-kama. Ya ce akwai bukatar shugaban kasa yazo daga kudu.

A bangare guda, Gwamnan jihar Zamfara, Mohammad Bello Matawalle, ya bayyana cewa akwai kimanin yan bindiga 30,000 a jiharsa da kuma wasu jihohin Arewacin Najeriya biyar.

A cewar gwamnan, akwai akalla sansanonin tsagerun yan bindiga 100 kuma kowace sansani na da akalla yan bindiga 300.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin sabon kwamishanan labaransa, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara, a hira da manema labarai ranar Juma'a a jihar Kaduna, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng