"Bai Son Wawushe Kudin 'Yan Najeriya"; Matar Atiku Ta Bayyana Abin da Mijinta Yake Nema

"Bai Son Wawushe Kudin 'Yan Najeriya"; Matar Atiku Ta Bayyana Abin da Mijinta Yake Nema

  • Titi Abubakar, matar ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ta ce mijinta ba ya neman kuɗin ’yan Najeriya
  • Ta ce Atiku Abubakar na son saka wa al’umma kan abin alherin da Najeriya ta yi masa idan aka zaɓe shi a 2027
  • Titi ta bayyana Atiku a matsayin mai taimakawa marasa karfi kuma gogaggen ɗan siyasa da ba zai fara koyon mulki ba idan ya ci zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Titi Abubakar, matar ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ta ce mijinta ba ya neman kuɗin ’yan Najeriya.

Titi Abubakar ta bayyana cewa mijin nata yana son ya yi wa al’umma hidima idan aka zaɓe shi a 2027.

Titi ta yi magana kan Atiku Abubakar
Titi tare da mijinta Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Titi ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da shafin TV Platinum ya wallafa a X ranar Juma’a, inda aka gan ta tana yi wa mijinta kamfen a wani taron gangami.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ki karbar tayin zama abokin takarar Atiku a ADC? An ji gaskiyar zance

Titi ta yaba wa Atiku

Matar tsohon mataimakin shugaban ƙasar ta bayyana Atiku a matsayin mai taimakawa marasa karfi kuma gogaggen ɗan siyasa wanda ba zai buƙaci koyon aikin gwamnati ba idan aka zaɓe shi.

“Atiku mutum ne da za a iya tallata shi cikin sauki. Shi ya sa nake alfahari da mijina sosai. Atiku mai taimako ne. Atiku ya taɓa yin hakan a baya. Atiku ba zai fara koyon aikin ba, kuma Atiku ba sabon shiga ba ne.” In ji ta

Atiku ba ya neman kuɗi

Matar jigon a ADC ta yi watsi da zargin cewa mijinta, wanda zai cika shekara 80 a bana, har yanzu yana da burin tara dukiya ko neman mulki domin kashin kansa.

Ta dage cewa manufar tsohon mataimakin shugaban kasar ita ce yi wa al’umma hidima.

“Atiku ba ya son kuɗin ’yan Najeriya. Atiku kawai yana son ya mayar wa al’umma abin da al’umma ta yi masa. Domin mutane da yawa suna ci gaba da cewa, me yake nema? Ba da daɗewa ba zai cika shekara 80.” In ji ta

Kara karanta wannan

Peter Obi ya kinkimo maganar kisan Sardauna, ya bayar da shawara

Titi ta yi hasashen Atiku ya yi wa’adi biyu

Titi ta ƙara da cewa mijinta yana son koyar da matasan Najeriya yadda ake tafiyar da harkokin siyasa da mulki.

Ta kuma yi hasashen cewa daga baya ’yan Najeriya za su nemi ya sake tsayawa takara a karo na biyu, duk da cewa a baya ya nuna cewa zai yi wa’adi ɗaya ne kacal.

“Atiku yana son ya koyar da ku, yara, yadda ake tafiyar da siyasa. ’Yan Najeriya za su riƙa marmarin Atiku a karo na biyu, duk da cewa ya ce zai yi sau ɗaya ne kawai. Amma ’yan Najeriya za su nemi ya dawo su kawo shi.” In ji ta.

Daga bisani, Titi ta koka kan halin da tattalin arzikin ƙasar da shugabanci suka shiga a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.

Matar Atiku ta yabi mijinta
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Batun Obi ya ki karbar tayin Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya musanta batun cewa ya ƙi karbar tayin zama abokin takarar Atiku Abubakar, a zaɓen 2027.

Peter Obi ya ce ba a taɓa yi masa irin wannan tayin ba, don haka ba zai yiwu ya ƙi wata shawara da ba a gabatar masa da ita ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng