Duba garejin dan wasan kwallo Obafemi Martins, mai dauke da kasaitattun motocin kece raini
- Obafemi ya kayatar da mabiyansa na shafin sada zumunta da hadadden garejinsa
- A hoton da ya wallafa, an ga motoci biyu kirar Bentley Bentayga daga cikin jerin motocin
- An gano cewa Martinsa ya tara dukiyar da ta kai dala miliyan 35 wanda daidai yake da N13.4 biliyan
Obafemi Martins ya bayyana gagagrumin garejinsa ta hanyar wallafa hotunan a kafar sada zumuntar zamnai. An hango motoci kirar Bentley Bentayga a wani sashin.
An gano cewa Martins ya mallaki motar kirar 2017 wacce kudinta kadai ya kai naira miliyan 88 tun a wasu shekaru da suka gabata. Hoton kuwa ya nuna motocin har biyu.
Har a yau mota kirar Bentley Bentayga tana daya daga cikin motoci masu matukar gudu, mai tsada da kuma alfarma a kasuwa.
Martins ya saka kwallo 18 a raga a cikin fitowa 42 da yayi a Najeriya tsakanin 2014 zuwa 2015. A halin yanzu yana wasa ne a wata kungiyar kwallon kafa ta China mai suna Wuhan Zall.
Dukiyarsa kuwa ta kai dala miliyan 35 wanda yayi daidai da naira biliyan 13.4 kuma dan wasan kwallon kafa ne wanda ke son kayan alatu.
KU KARANTA: Da duminsa: Jigo a fadar Buhari ya rasu sakamakon ciwon kansa
KU KARANTA: Hotunan matashi mai shekaru 35 ya yi wuff da tsohuwa mai shekaru 80
A wani labari na daban, Major, karen Joe Biden ne dabba na farko mara gata da zai fara rayuwa a cikin white house, The Cable ta wallafa.
Ana sa ran karen dan asalin kasar Jamus zai koma rayuwarsa tare da Biden da Jill, matarsa da zarar an rantsar dashi sun koma White House.
Kamar yadda Sky News suka ruwaito, ba wannan ne karo na farko da kare ya fara rayuwa a White House ba, Major ne kare na farko wanda aka dauko daga makwancin karnuka da zai zauna a nan.
Champ ya fara rayuwa tare da iyalin Biden a 2008, shekarar da ya zama mataimakin shugaban kasa Barack Obama.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng