INEC Ta Saɓa da Peter Obi na Shirin Yi Mata Kishiya a Zaben Shekarar 2027
- INEC ta sake jaddada cewa ita ce kadai ke da ikon tattarawa da sanar da sakamakon zabe yayin da ake shirin zaben 2027
- Jam’iyyar ADC ta goyi bayan shirin Obi na tattara sakamakon rumfunan zabe daban, domin kwatanta bayanan da INEC za ta sanar
- Masana fasaha sun ce tsarin na iya aiki, amma rashin intanet, matsalar tsaro, bayanan bogi da yiwuwar rikita alkaluman zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta sake jaddada cewa ita ce kadai ke da hurumin tattarawa da sanar da sakamakon zabe a Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da jam’iyyun adawa ke shirin samar da hanyoyin da za su rika bibiyar sakamakon rumfunan zabe a zaben 2027.

Source: Twitter
Abin da Obi ya ce kan sakamakon zaben 2027
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya gabatar da shawarar samar da wani tsari na daban domin tattarawa da aika sakamakon zabe, cewar Leadership.
Obi ya ce kungiyar yakin neman zabensa za ta iya karbar sakamakon rumfunan zabe zuwa cibiyarta, tare da aika su zuwa tsarin INEC na hukuma.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Arise TV ranar Alhamis, inda ya ce tsarin zai taimaka wajen tabbatar da sahihancin sakamakon da aka samu.
Obi ya ce tawagarsa za ta samar da abin da ya kira tsarin “aika sakamako ta hanyoyi biyu”, inda za a tura bayanai ga INEC da cibiyarsu, cewar Punch.
Ya ce:
“Dole ne mu tabbatar cewa a kowace rumfar zabe, an kirga kuri’u, an rubuta kuri’u yadda ya kamata, sannan an aika da sakamakon yadda ya dace.”
Tsohon gwamnan Anambra ya ce tsarin ba zai maye gurbin tsarin INEC ba, sai dai zai samar da wata hanya ta karin sa ido kan sahihancin sakamakon.
Shirin Obi ya samo asali ne daga rashin amincewa da wasu matakan INEC, musamman bayan matsalolin da aka samu da tsarin IReV yayin zaben shugaban kasa na 2023.
A zaben 2023, hukumar INEC ta sanar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara, yayin da kotuna suka tabbatar da sakamakon zaben.
Sai dai Obi da magoya bayansa sun ci gaba da cewa shi ne ya lashe zaben, amma aka hana shi samun nasarar.
A wani bangare, jam’iyyar ADC ta ce ita ma ba za ta dogara kacokan da INEC wajen tattara nata sakamakon zaben 2027 ba.

Source: Facebook
Tattara sakamako kai tsaye ba sauya INEC ba
Muhimmancin samun hanyoyi masu zaman kansu na tattara bayanai na kara jaddada cewa za a iya inganta gaskiyar sakamakon zabe idan bangarori masu zaman kansu suka adana bayanan abubuwan da suka faru a rumfunan zabe.
Sai dai masana na ganin nasarar irin wannan shiri za ta dogara ne da yadda za a dauke shi a matsayin hanyar tabbatar da sahihancin sakamako, ba wata madadin hukumar zabe ba.
Yayin da INEC ke da alhakin gudanar da zabe, kula da tsarin tattara sakamako da sanar da wanda ya yi nasara, jam’iyyar siyasa ba za ta iya karbe wadannan nauyin doka ta hanyar amfani da fasaharta ba.

Kara karanta wannan
'Abin da tsofaffin shugabanni ke tsoro Tinubu ya aiwatar saboda tausayin 'yan kasa'
Abin da jam’iyya za ta iya yi shi ne adana bayanan da wakilanta suka tattara da kansu kan abubuwan da suka gani tare da rubuta bayanan da suka samu a rumfunan zabe.
Masana sun ce irin wannan tsari zai iya taimakawa wajen tabbatar da gaskiyar sakamakon zabe, muddin aka yi amfani da shi wajen tantance bayanai.
Sun ce INEC ce ke da alhakin gudanar da zabe, tattara sakamakon hukuma da sanar da wanda ya lashe zabe, kuma jam’iyya ba za ta iya karbe wadannan hurumai ba.
Obi ya yi magana kan kin takara da Atiku
A wani labarin, an ji cewa Peter Obi ya yi magana kan batun cewa ya ki karbar tayin zama abokin takarar Atiku Abubakar a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.
Ɗan takarar na NDC ya ce batun haɗin gwiwar ’yan adawa ya kamata ya shafi jam’iyyun siyasa, ba tattaunawar ’yan siyasa guda biyu kawai ba.
Obi da Atiku sun kasance cikin hadakar ’yan adawa da ta haɗa kai a ƙarƙashin ADC a 2025, kafin daga bisani kowannensu ya fito a matsayin ɗan takarar wata jam’iyya.
Asali: Legit.ng

