Kafin 2027, INEC Ta Saka Ranar Zabe a Gombe da Wasu Jihohi 3

Kafin 2027, INEC Ta Saka Ranar Zabe a Gombe da Wasu Jihohi 3

  • Hukumar INEC ta kayyade ranar 19 ga Satumba domin gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabu guda biyar a jihohin Gombe, Kano, Bauchi da Delta
  • Rahoto ya nuna cewa za a gudanar da zaɓen ne a mazabar tarayya guda ɗaya da kuma mazabu huɗu na majalisun dokokin jihohi
  • INEC ta ce zaɓen zai maye gurbin kujerun da suka zama babu kowa, ciki har da kujerar Gombe/Kwami/Funakaye da marigayi Yaya Bauchi Tongo ya riƙe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanar da ranar 19 ga Satumba a matsayin ranar gudanar da zaɓe a mazabu guda biyar a jihohin Gombe, Kano, Bauchi da Delta.

Babban Sakataren Yaɗa Labarai ga Shugaban INEC, Mista Tunde Oketola, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu

Mutane a wajen zabe
Yadda aka yi zaben gwamna a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Oketola ya bayyana cewa zaɓen zai ƙunshi mazabar tarayya guda ɗaya da kuma mazabu huɗu na majalisun dokokin jihohi.

Jihohin da za a yi zabe

A Gombe, za a gudanar da zaɓen ne a mazabar Gombe/Kwami/Funakaye ta tarayya domin cike kujerar da marigayi Hon. Yaya Bauchi Tongo ya bari bayan rasuwarsa.

A Bauchi kuma, INEC ta ware mazabun Disina da Sakwa na majalisar dokokin jihar domin gudanar da zaɓen.

Haka kuma, za a gudanar da zaɓen a mazabar Udu ta jihar Delta da kuma mazabar Dawakin Kudu ta jihar Kano.

Dalilin yin zabe a Gombe

Yaya Bauchi Tongo, wanda ya wakilci mazabar Gombe/Kwami/Funakaye a Majalisar Wakilai, ya rasu ne ranar Juma'a, 12 ga Yuni, 2026, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

The Cable ta wallafa cewa an haifi Tongo a ranar 18 ga Yuni, 1963, a Ƙaramar Hukumar Funakaye ta Jihar Gombe. Ya fara harkar siyasa a shekarar 1999 a matsayin kansila a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Kungiyar APC ta cika umarnin Shettima, ta dauki nauyin marayu 60

Daga shekarar 2007 zuwa 2009, ya kasance mai ba gwamnan Gombe shawara kan ƙananan hukumomi da harkokin siyasa.

Daga baya ya zama ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe mai wakiltar Funakaye ta Kudu a shekarar 2011, kafin daga bisani ya koma Majalisar Wakilai a shekarar 2015.

Wajen da ake zabe a Osun
Jami'an INEC a wajen da ake zabe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

An sake zaɓar Tongo a Majalisar Wakilai a shekarar 2023 a ƙarƙashin PDP, kafin ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC a watan Maris na 2026.

INEC na shirin zaben 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta ce za ta ƙaddamar da wani sabon tsarin sa ido kan shirye-shiryen zaɓen 2027 da zai bai wa hukumar damar bibiyar matakan shirye-shiryen zaɓe a dukkan jihohi 36.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne yayin buɗe wani taron bita na kwana biyu ga Sakatarorin Gudanarwa na hukumar da aka gudanar a otal ɗin Marriott da ke Ikeja, Lagos.

Ya ce taron zai samar da wani tsari na bai ɗaya na bibiyar ayyukan Sakatarorin Gudanarwa, wanda za a haɗa kai tsaye da cibiyar sa ido da tallafa wa zaɓe da kuma tsarin gudanar da ayyukan zaɓe na hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng