Datti Baba Ahmed Ya Fadi Mummunan abin da Gwamnatin Buhari Ta Fi Saura

Datti Baba Ahmed Ya Fadi Mummunan abin da Gwamnatin Buhari Ta Fi Saura

  • Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mafi cin hanci da rashawa da Najeriya ta taɓa gani
  • Datti ya ce duk wata manufar tattalin arziki ba za ta yi nasara ba idan cin hanci da rashawa ya yi katutu a cikin gwamnati
  • Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ya kuma soki yadda gwamnatin Buhari ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya yi magana kan gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

Datti Baba-Ahmed ya bayyana gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mafi cin hanci da rashawa da Najeriya ta taɓa fuskanta.

Datti Baba-Ahmed ya soki gwamnatin Buhari
Tsohon shugaban kasa Muhammadu da Yusuf Datti Baba-Ahmed Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Datti ya yi magana kan gwamnatin Tinubu

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin MIC On Podcast With Seun Okinbaloye.

Kara karanta wannan

Tinubu bai cire kansa ba, ya faɗi irin shugabannin da Najeriya ke buƙata

An tambaye shi ra’ayinsa kan manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman cire tallafin man fetur da haɗa kasuwar canjin kuɗin waje.

Sai dai Datti ya mayar da hankali kan batun cin hanci, yana mai cewa babu wata manufar tattalin arziki da za ta yi nasara idan cin hanci ya zama ruwan dare a gwamnati.

“Duk wata manufa, komai kyawunta, idan aka gauraya ta da cin hanci, ba za ta taɓa aiki ba,” in ji shi.

Ya zargi gwamnatin Buhari da cin hanci

Da yake bayyana dalilin da ya sa yake ganin gwamnatin Buhari ta gaza, Datti Baba-Ahmed ya danganta abin da ya kira gazawar tsohon shugaban ƙasar da cin hanci da rashawa.

“Me ya sa Buhari ya gaza sosai? Saboda cin hanci ne, ina ba da haƙuri. Allah ya ji ƙansa. Dukkanmu muna kan wannan tafiya, kuma za mu tafi mu ba da bayanin abin da muka aikata,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Abin da zai faru da masu zagi da sukar gwamnatin Tinubu

Datti ya ƙara da yin kakkausar suka ga gwamnatin Buhari, yana mai cewa bai taɓa ganin gwamnati mai irin wannan matakin cin hanci da rashawa da rashin ɗa’a ba.

“Ba a taɓa samun gwamnati mai cin hanci kamar gwamnatin Buhari ba, kuma ba a taɓa samun gwamnati marar ɗa’a kamar gwamnatin Buhari ba,” in ji shi.

Ya koma kan zaɓen 2023

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ya kuma danganta sukar da yake yi wa gwamnatin Buhari da yadda aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya zargi gwamnatin da gaza cika alkawarin da ta yi na tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci, wanda zai kasance cikin ’yanci da adalci.

A cewarsa, Buhari ya yi alkawarin cewa zaɓen 2023 zai kasance cikin ’yanci da adalci, amma abubuwan da suka faru wajen aika da sakamakon zaɓe da tattara ƙuri’u sun haifar da tambayoyi.

Muhammadu Buhari ya sha suka a wajen Datti Baba-Ahmed
Tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Babachir ya yi magana kan Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya yi magana kan yakin neman zaben Marigayi Muhammadu Buhari a 2015.

Babachir Lawal ya ce Shugaba Bola Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen daukar nauyin yakin neman zaben marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng