'Zan Ji Tsoron Ubangiji a Mulki na': Ɗan Takarar Gwamnan APC Ya Roki Alfarma
- Dan takarar gwamnan APC a Rivers, Kingsley Chinda, ya fara kamfen ɗinsa, inda ya yi alkawarin samar da ci gaba ga al'ummar jihar
- Chinda, wanda ke da kusanci da Nyesom Wike, ya lashe zaɓen fidda gwani na APC ba tare da hamayya ba, bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya janye
- Fubara ya bayyana goyon bayansa ga Chinda a watan Yuli, bayan sulhunsu da Wike, wanda ya biyo bayan sauya sheƙar gwamnan daga PDP zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rivers - Dan takarar gwamnan APC a Rivers, Kingsley Chinda ya kaddamar da kamfen dinsa na zaɓen shekarar 2027.
Chinda ya yi alkawarin yi wa jihar hidima “da tsoron Ubangiji da ƙaunar ɗan Adam” idan aka zaɓe shi.

Source: Twitter
Chinda, wanda ke da kusanci da Nyesom Wike, ministan Abuja, ya bayyana hakan a wani gajeren saƙo da ya wallafa a X, tare da hoton da ya nuna fara kamfen ɗinsa.

Kara karanta wannan
Da gaske Akpabio ya yi wa 'yan Arewa barazanar shan azaba idan Tinubu ya fadi a 2027?
Chinda ya yi alkawura ga yan Rivers
Saƙon nasa ya zo ne yayin da kamfen ɗin zaɓen gwamna da na majalisun dokokin jihohi a faɗin ƙasar ya fara a hukumance, bisa jadawalin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
Ya ce:
“Za mu yi wa Rivers hidima da tsoron Ubangiji da ƙaunar ɗan Adam."
Chinda, tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai kuma ɗan takara tilo, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC a watan Mayu.
Hakan ya biyo bayan janyewar Siminalayi Fubara, gwamnan Rivers mai ci, daga takarar. Da farko an tantance Fubara tare da Chinda domin shiga zaɓen fidda gwani na APC.
Sai dai Fubara ya janye daga takarar, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne bisa ga ƙudirinsa da kuma sadaukarwa domin zaman lafiya da haɗin kan Rivers.
A watan Yuli, Fubara ya bayyana goyon bayansa ga Chinda, inda ya bayyana shi a matsayin wanda yake so ya gaje shi a matsayin gwamna.
Gwamnan ya kuma goyi bayan Rainbow Coalition, wata ƙungiyar siyasa da ministan Abuja ya kafa a Rivers domin neman wa Shugaba Bola Tinubu wa’adi na biyu.
Fubara da Wike sun shafe lokaci mai tsawo suna rikicin siyasa, lamarin da ya haifar da yunƙurin tsige gwamnan daga muƙaminsa da ’yan majalisar da ke biyayya ga ministan Abuja suka yi.
Daga bisani, ɓangarorin biyu sun cimma matsayar sulhu ta siyasa, sannan daga baya suka sake kulla kyakkyawar alaƙa bayan Fubara ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa APC.
Chinda ya yi murabus a majalisar wakilai
An ji cewa dan takarar gwamnan jihar Rivers na jam'iyyar APC, Hon. Kingsley Chinda ya ajiye mukamin shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai.
Chinda ya sanar da haka ne a takardar da kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya karanta, inda ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC.
Tun farko dan Majalisar, wanda ke da alaka ta siyasa da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a jihar Rivers.
Asali: Legit.ng
