Wata Sabuwa: An Dauko Abin da Ya Faru a Mulkin Buhari Fiye da Shekara 1 bayan Ya Bar Duniya
- Sanata Shehu Sani ya kalubalanci ’yan Arewa masu sukar gwamnatin yanzu kan rashin tsaro, yana mai tunatar da su abin da ya faru a mulkin Buhari
- Tsohon ɗan majalisar ya yi gargadin kada ’yan siyasa su mayar da rashin tsaro, ƙabila da addini makamai wajen neman goyon bayan siyasa
- Shehu Sani ya ce ya kamata a riƙa tantance gwamnatoci bisa ayyukansu, ba bisa ƙabila, addini ko jam’iyyar siyasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria – Sanata Shehu Sani ya kalubalanci ’yan Arewa masu sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalar rashin tsaron da ta addabi Najeriya.
Sanatan ya bayyana cewa gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta shafe shekara takwas tana mulki ba tare da kawo ƙarshen ’yan bindiga da ta’addanci a Arewa ba.

Source: Facebook
Leadership ta ce Sani ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, inda ya gargadi ’yan siyasa kan amfani da rashin tsaro, ƙabilanci da addini a matsayin makamai wajen tara goyon bayan
Shehu Sani ya soki ’yan siyasa
Tsohon ɗan majalisar dattawan ya ce bai dace ’yan siyasar da suka taɓa mulki a baya su gabatar da kansu a matsayin masu ceto da za su iya magance matsalolin tsaron Najeriya ba.
Ya ce Arewa ta fuskanci munanan hare-hare, kashe-kashe, satar mutane, fyade, lalata al’ummomi da raba dubban mutane da muhallansu a ƙarƙashin gwamnatocin da suka gabata.
Ya ce rashin tsaro yana shafar ’yan Najeriya ba tare da la’akari da addininsu ko ƙabilarsu ba, don haka ya kamata a tunkare shi tare.
Ya dauko batun mulkin Buhari
Ya bayyana cewa a lokacin gwamnatin Buhari, ’yan Arewa ne suka riƙe wasu daga cikin muƙaman tsaro mafi muhimmanci, cewar rahoton Punch.
Ya lissafa Shugaban Hafsoshin Tsaro, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Shugaban Rundunar Sojin Sama, Shugaban Rundunar Sojin Ruwa da Ministan Tsaro, da sauransu.
Shehu Sani ya kuma ambaci tsohon Sufeto-Janar na ’yan sanda Ibrahim Idris, tsohon Darakta-Janar na Hukumar DSS Lawal Daura da sauran manyan jami’an tsaro da na leƙen asiri.

Source: Facebook
Ya ce duk da yawan ’yan Arewa da suka riƙe muƙaman tsaro masu muhimmanci, matsalar ’yan bindiga da ta’addanci ta ci gaba da zama babbar barazana a yankin.
Shehu Sani ya ce:
“Idan ka duba tsarin tsaro a ƙarƙashin Buhari, da yawa daga cikin mutanen da suka riƙe muƙaman da suka fi muhimmanci ’yan Arewa ne, amma duk da haka, Buhari bai kawo ƙarshen ’yan bindiga ko ta’addanci a Arewa ba.”
Sani ya ce saboda haka ya kamata ’yan Najeriya su riƙa tantance gwamnatoci bisa irin ayyukan da suka yi, ba bisa ƙabila, addini ko alaƙar siyasa ba.
Shehu Sani ya soki shirin Atiku
Kun ji cewa Shehu Sani ya bayyana alkawarin Atiku na dawo da tallafin man fetur a matsayin yaudara da kuma manufar da ba za ta dore ba.
Tsohon sanatan ya ce Najeriya ba za ta iya komawa tsarin tallafin man fetur da ya ce ya jawo kashe tiriliyoyin Naira tare da kara matsalolin cin hanci da fasa-kwaurin man fetur ba.
Asali: Legit.ng


