Zaben Amurka Ya Firgita Trump, zai Raba Miliyoyi don a Zabi Dan Takararsa
- Shugaban kasa Donald Trump ya yi alƙawarin raba dalar Amurka 5,000 ga kowane ɗan kasar idan RNC ta riƙe majalisu
- Trump ya bayyana wannan alƙawari ne a daren farko na taron jam'iyyar Republican domin ƙarfafa gwiwar masu ƙada ƙuri'a
- Shugaban ya kuma buƙaci magoya bayansa da su kaddara cewa yana cikin 'yan takara a zaɓen kasar da ke tafe a watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wani alƙawari ba da $5,000 da 'yan Amurka idan har jam'iyyar Republican ta sami nasarar riƙe majalisar wakilai da ta dattawa a zaɓen watan Nuwamba.
Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a daren farko na taron jam'iyyar Republican (RNC), inda yake ƙoƙarin tabbatar da cewa jam'iyyarsa ta ci gaba da riƙe iko da madafun iko.

Kara karanta wannan
Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya

Source: Getty Images
Trump zai raba kudi
CNN ta ruwaito cewa Trump bai fadi dalla-dalla yadda zai samo wadannan kudi ba, amma ya kwatanta matakin da rabon ribar da kamfanoni ke yi wa masu hannun jari.
Ya rubuta cewa:
"Wannan shi ne alƙawarina: Idan 'yan jam'iyyar Republican suka sami nasara a majalisar wakilai da kuma majalisar dattawan Amurka, duka biyun, zan rarraba dalar Amurka 5,000 ga kowane ɗan ƙasa baligi a Amurka."
Trump ya soki 'yan adawa
A lokacin jawabin nasa da ya kammala daren farko na taron, Trump ya caccaki ƴan jam'iyyar Democrat, inda ya fake da kiyaye tsaron iyakoki da kuma adawarsa da shigar mata masu sauyin halitta a harkar wasannin mata.
BBC ta wallafa cewa ya bayyana cewa zai fita yaƙin neman zaɓe ka'in da na'in tare da ƴan takara guda 35 na majalisa domin tabbatar da cewa jam'iyyar ta sami nasara.

Source: Getty Images
"Ina buƙatar ku ɗauka kamar ina takara ne,"
In ji Trump lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi.
Trump ya kuma buƙaci al'ummar jihar Texas da su haɗu waje guda domin goyon bayan Ken Paxton, lauyan gwamnati na jam'iyyar Republican wanda ya kayar da Sanata John Cornyn a zaɓen fitar da gwani.
Batun nukiliyar Iran
A wani labarin, kun ji cewa mambobin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) sun gudanar da ƙuri'ar mika batun nukiliyar kasar Iran zuwa ga Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Rahoto ya nuna cewa an amince da wannan ƙuduri ne sakamakon ƙuri'u 23 da suka goyi baya, yayin da ƙasashe uku suka ƙi amincewa, sannan ƙasashe takwas suka janye jikinsu daga ƙuri'ar.
Wannan ne karon farko cikin shekaru 20 da aka mika batun Iran ga kwamitin tsaro saboda gaza cika tsarin bayar da rahotannin ayyukan makamashin nukiliyarta, yayin da Iran din ta yi alhinin matakin tare da bayyana shi a matsayin na siyasa.
Asali: Legit.ng
