'Dalilin da Ya Kamata Ya Sa 'Yan Arewa Su Ki Zabar Tinubu a 2027'

'Dalilin da Ya Kamata Ya Sa 'Yan Arewa Su Ki Zabar Tinubu a 2027'

  • Ken Imasuagbon, jigon ADC, ya yi kira ga ’yan Arewa su yi amfani da ƙarfin yawansu wajen kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Imasuagbon ya buƙaci ’yan Najeriya su goyi bayan Atiku Abubakar, yana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai iya haɗa kan ƙasar
  • Ya ce shirin tattalin arzikin Atiku ya haɗa da sake buɗe iyakokin Najeriya domin bunƙasa kasuwanci da rage tsadar kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Gabanin babban zaɓen 2027, wani jigon jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Barrister Ken Imasuagbon, ya yi kira ga ’yan Arewa kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.

Ken Imasuagbon ya yi kira ga 'yan Arewa da su yi amfani da ƙarfin yawansu wajen kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

An bukaci 'yan Arewa su ki zabar Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Imasuagbon ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da ya rabawa ’yan jarida a Benin, babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Tinubu bai cire kansa ba, ya faɗi irin shugabannin da Najeriya ke buƙata

Ya buƙaci ’yan Najeriya su haɗa kai wajen mara wa ɗan takarar ADC kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, baya.

Ya ce Atiku zai iya ceto Najeriya

Imasuagbon ya ce ya kamata ’yan Najeriya su goyi bayan Atiku domin ceto ƙasar daga matsalar tattalin arziki da yake cewa ta addabi al’umma.

Ya bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin jagoran da zai iya haɗa kan ’yan Najeriya tare da rage rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa da zamantakewa.

A cewarsa, Atiku gogaggen ɗan siyasa ne kuma mutum mai daidaito wanda ba zai ba ’yan Najeriya kunya ba idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar.

Ya ce Atiku zai magance talauci da yunwa

Jigon ADC ya ce Najeriya na ci gaba da fama da manyan matsalolin tsari da kuma tsananin rayuwa.

Ya yi amanna cewa Atiku na da ƙwarewar jagoranci da za ta taimaka wajen karya shingen talauci da yunwa da ke addabar al’ummar ƙasar.

Kara karanta wannan

Tsakanin Atiku da Obi waye zai iya ƙalubalantar Tinubu? an fadi wanda ya zo da gaske

Imasuagbon ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai iya taimakawa wajen kawo ƙarshen matsalolin tattalin arziki da rarrabuwar kawuna da ya ce Najeriya ke fama da su tun bayan samun ’yancin kai.

An buƙaci sake buɗe iyakokin ƙasa

Ya ce ɗaya daga cikin muhimman manufofin tattalin arzikin Atiku a ƙarƙashin tutar ADC shi ne sake buɗe iyakokin Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen bunƙasa kasuwancin yankin da kuma ƙara inganta harkokin cinikayya tsakanin Najeriya da sauran ƙasashen Yammacin Afirka.

Imasuagbon ya ce rufe iyakokin ya cutar da ’yan kasuwa masu gudanar da harkokin kasuwanci bisa doka, tare da taimakawa wajen ƙara tsadar kayan abinci.

Ya ce sake buɗe iyakokin zai iya taimakawa wajen rage farashin kayayyaki da ayyuka ga ’yan Najeriya.

Ya soki cire tallafin man fetur

Imasuagbon ya kuma ce shirin tattalin arzikin Atiku zai mayar da hankali kai tsaye kan matsalar tsadar rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Ya ce Atiku ya yi alƙawarin sauya matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar.

A cewarsa, wannan na daga cikin matakan da Atiku zai ɗauka domin rage matsin tattalin arziki da sauƙaƙa wa ’yan Najeriya halin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Okonkwo ya haska dalilin da ya sa ba a son Atiku ya zama shugaban kasa

Shugaba Tinubu na neman tazarce a zaben 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ofis Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Remi na son a sake zaben Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta roƙi yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen mijinta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Remi Tinubu ta ce tana son jin daɗin Najeriya mai kyau a lokacin tsufa, tana mai cewa ita da shugaban ƙasa suna ƙoƙarin inganta ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng