Matasan da Ake Zargi da Tare Peter Obi Sun Shiga Matsala, An Kwantar da Mutum 10 a Asibiti
- An kai matasa sama da 10 da ke zargi asibitin koyarwa na jihar Benue bayan harin da aka kai wa ayarin dan takararw NDC, Peter Obi
- Rahotanni sun ce wasu da ake zargin yan daba ne sun kai hari kan ayarin Obi a hanyar Gboko zuwa Makurdi
- Jam'iyyar NDC ta ce daya daga cikin wadanda suka ji rauni ya mutu, amma asibiti bai tabbatar da hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Makurdi, Benue - An kai matasa sama da 10 asibitin koyarwa na jami'ar jihar Benue (BSUTH) da ke Makurdi domin jinya bayan harin da aka kai wa ayarin dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi.
Rahotanni sun ce ana zargin matasan da ke karbar magani a asibitin na da hannu a harin da yan daba suka kai kan ayarin Obi a hanyar Gboko zuwa Makurdi ranar Talata.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya fito ya fadi gaskiya, ya ce abin da aka yi wa Peter Obi bai dace ba

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa harin ya hana dan takarar shugaban kasar ci gaba da tafiya zuwa Yelwata da ke karamar hukumar Guma.
Peter Obi ya nufi Yelwata
An ce Obi na kan hanyarsa ta zuwa Yelwata ne domin jajanta wa wadanda harin yan ta'adda na ranar 13 ga watan Yunin 2025 ya Peter lokacin da lamarin ya faru.
Bayan harin, dan takarar shugaban kasa na NDC ya zargi mai taimaka wa Gwamna Hyacinth Alia kan harkokin matasa da shirya harin.
Obi ya kuma yi zargin cewa an tara wasu matasa domin tare masa hanya da hana shi wucewa bayan ya isa Makurdi, babban birnin jihar Benue, kafin ya nufi Yelwata inda aka kai wa ayarinsa hari.
Asibiti ya tabbatar da kai matasa
Wani jami'in BSUTH da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar a yau Laraba cewa an kai matasa sama da 10 asibitin domin samun kulawar gaggawa.
Sai dai jami'in ya ce bai da tabbacin ko wadanda aka kawo asibitin suna da alaka da harin da aka kai wa ayarin Peter Obi.
NDC ta ce mutum daya ya mutu
Sakataren yada labarai na NDC a jihar Benue, Agile-Bem Jabez Ordedoo, ya yi ikirarin cewa daya daga cikin wadanda ake zargin sun kai harin ya mutu yayin karbar magani a asibitin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Ordedoo ya ce:
"Muna bakin cikin sanar da ku cewa daya daga cikin matasan da aka dauki nauyinsu domin kai hari kan dan takarar shugaban kasa da dan takarar gwamnan NDC ya rasu da safiyar yau a asibitin koyarwa da ke Makurdi."
Ya kara da cewa an kai gawar mutumin dakin ajiye gawa, yayin da sauran wadanda suka ji rauni ke kwance cikin mawuyacin hali a sashen gaggawa na asibitin.
Gwamnatin Benue ta soki Peter Obi
Kun ji cewa Gwamnatin Benue ta zargi Peter Obi da neman tayar da hankali, bayan da aka toshe ayarin motocinsa yayin ziyararsa jihar a jiya Talata.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Solomon Iorpev, ya ce Obi bai sanar da gwamnatin jihar a hukumance kafin ziyarar ba, wanda ya saba ka’idojin aiki
Asali: Legit.ng
