Musulmi da Kirista Sun Ƙulla Yarjejeniya yayin da Ake Hasashen Rikici a Zaɓen 2027

Musulmi da Kirista Sun Ƙulla Yarjejeniya yayin da Ake Hasashen Rikici a Zaɓen 2027

  • Al'ummar Kiristoci da Musulmai matasa a Najeriya sun shirya tunkarar zaben shekarar 2027 da ke tafe a Najeriya
  • Shugabannin matasan sun bukaci matasa su guji shiga harkar bangar siyasa, karɓar kuɗin saye ƙuri’a da duk wani aiki da ka iya jefa ƙasa cikin rikici
  • Sun kuma jaddada cewa haɗin kan Musulmai da Kiristoci zai taimaka wajen yaƙi da barazanar tsaro da kuma gina Najeriya mai zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Matasan ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (YOWICAN) da Majalisar Ƙungiyoyin Matasa Musulmai ta Ƙasa (NACOMYO) sun gana a Abuja.

Kungiyoyin addinan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin babban zaɓen 2027.

Kirista da Musulmi sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya
Shugabannin matasan Kiristoci da Musulmi yayin yarjejeniyar zaman lafiya. Hoto: Youth Council of Nigeria.
Source: Facebook

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a Cibiyar Kiristoci ta Ƙasa da ke Abuja ranar Juma’a, yayin taron matasan Kiristoci na ƙasa kan tsaro na 2026 da kuma ibadar godiya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ADC ta fitar da sunayen 'yan takararta na gwamna a jihohi 28

Majiyoyi suka ce yarjejeniyar zaman lafiyar na da nufin ƙarfafa haƙurin addini, yin watsi da rikicin siyasa da kuma inganta zaman lafiya kafin zaɓen 2027

Taron na tsawon kwanaki uku ya haɗa jami’an tsaro, wakilan gwamnati, shugabannin coci-coci da matasa daga jihohi 36, Babban Birnin Tarayya (FCT), ƙungiyoyin CAN biyar da shiyyoyin siyasa shida

A cikin jawabin maraba da mahalarta taron, shugaban ƙasa na YOWICAN, Ven. Evang. Ademola Arowolo, ya bayyana yarjejeniyar zaman lafiyar a matsayin “alkawarin fata da sanarwar haɗin kai” da aka tsara domin dakile rikicin zaɓe da saɓanin addinai daga matakin ƙasa har zuwa matakin ƙananan hukumomi.

Ya ce:

“Yau wata muhimmiyar rana ce a tarihin shigar matasa cikin harkokin ƙasa, shugabanci na addini, bayar da shawarar tsaron ƙasa da haɗin gwiwar addinai a Najeriya.
"Wannan yarjejeniyar zaman lafiya ta fi kasancewa takarda. Alkawarin fata ce, sanarwar haɗin kai da kuma alƙawarin Kiristoci da Musulmai matasa na aiki tare wajen inganta zaman lafiya, adalci, tattaunawa, haƙuri da ci gaban ƙasa.”

Da yake magana da manema labarai a wata hira, Arowolo ya jaddada muhimmancin kare rayukan mutane, inda ya bukaci matasa su ƙi shiga ta’addancin siyasa da sayen ƙuri’a yayin da ƙasar ke shirin shiga sabon zagayen zaɓe.

Kara karanta wannan

Tsakanin Atiku da Obi waye zai iya ƙalubalantar Tinubu? an fadi wanda ya zo da gaske

Shawarar shugaban CAN ga.matasa

Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Most Rev. Daniel Okoh, ya bukaci matasan Kiristoci su tashi tsaye wajen gina ƙasa tare da zama abin koyi na ɗabi’a

Okoh, wanda Rev. Simon Dolly-KIF, sakataren ƙungiyar shugabannin addinin Kirista na Arewa (NOCRELA), ya wakilta, ya bukaci matasa su wuce ƙalubalen da suka addabe su a baya

Ya ce:

“Lokaci ya yi da matasan Kiristocin Najeriya za su wuce iyakokin jiya, su rungumi nauyin gina Najeriya da muke son gani a gobe.
“Kada wani matashi Kirista ya zama kayan aikin tashin hankali, ƙiyayya, amfani da mutane ko lalata.
“Dole ne mu ƙi shiga duk wani abu da ke lalata rayuka da makomar ’yan Najeriya. Najeriya ta fi ƙabilarmu, ɗariƙarmu da bambancin siyasa girma.”

Hudubar Sultan ga Musulmi da Kirista

An ji cewa Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya buƙaci Musulmi da Kiristoci su daina aibanta addinan juna.

Mai alfarma Sultan ya gargadi mabiya addinai da kada wani bangare ya dauki kansa cewa ya fi abokin zamansa.

Sa’ad III ya jaddada muhimmancin kula da maƙwabta ba tare da la'akari da addininsu ko kabilar da suka fito ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.