An Yi Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Manoma da Makiyaya a Kudancin Najeriya

An Yi Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Manoma da Makiyaya a Kudancin Najeriya

  • Kungiyar manoma da makiyaya sun saka hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Kudancin Najeriya
  • Dokar wacce ta shafi yankin kudu maso yammacin Najeriya an tabbatar da ita ne a Ibadan hedikwatar jihar Oyo
  • Dukkan bangarorin sun amince da yarjejeniyar tare da bayyana yadda za ta yi tasiri a harkokin noma da kiyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kudu- Makiyaya da manoma sun saka hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Duk da cewa a shekarun baya ba a cika samun fada da rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin ba

Fulani da makiyaya
Manoma da makiyaya sun yi yarjejeniya a kudu domin kawo zaman lafiya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Amma karancin samun ciyawar dabbobi tare da bullowar fadace-fadace a yankin Arewacin kasar ya haifar da samun sabani tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

Kara karanta wannan

Dalibin da aka yi garkuwa da shi ya kubuta bayan kwanaki a jeji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da yake haifar da rikicin

Rikicin tsakanin manoma da makiyaya yawanci yana faruwa ne kan mallakar filaye da samar da abincin dabbobi.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa daga farkon shekarar 2018 zuwa yau sama da mutane 300,000 ne suka rasa gidajensu saboda rikicin a yankin.

Amma a wani yunkurin da ake ganin zai magance matsalar an samu yarjejeniya tsakanin makiyaya da manoma tun ranar 18 ga watan Afrilu.

Yarjejeniyar wacce aka kulla ta a Ibadan ta nuna cewa dukkan bangarorin sun yarda su yi aiki tare domin cigaban ƙasa baki daya.

Jawabin shugaban manoma

Shugaban kungiyar manoman yankin, Olusegun Dasaolu ya tabbatarwa 'yan jarida cewa wannan mataki ne mai matukar muhimmanci da suka dauka.

Ya kuma kara da cewa suna neman goyon bayan gwamnati a kan kudirin domin tabbatar da nasara da dorewarsa, cewar jaridar the Nation

Kara karanta wannan

'Ba zai tsinana komai ba', gamayyar 'yan siyasa sun soki Tinubu a ranar ma'aikata

A bangaren samar da wadataccen abinci kuwa, shugaban ya ce lalle yarjejeniyar ta zo dai-dai kan gaba domin manoma za su samu damar komawa gona cikin aminci.

Jawabin shugaban Miyetti Allah

Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, Othman Ngelzarma ya tabbatar da amincewa da yarjejeniyar.

Ya kuma kara da cewa hakan dama ce da suka samu wurin kawo tsaro ga manoma da makiyaya baki daya.

Rikicin manoma ya lakume rayuka a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa an samu sabani mara dadi tsakanin manoma da makiyaya a jihar Borno, an yi asarar rayuwa sama da biyar a rikicin.

Hakazalika, an ruwaito yadda aka kone gidaje sama da 40, lamarin da ya jawo shiga tsakani daga hukumomin tsaron jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel