Ana Maganar Hadaka, Obi da Kwankwaso Sun Ziyarci Abokin Takarar Atiku

Ana Maganar Hadaka, Obi da Kwankwaso Sun Ziyarci Abokin Takarar Atiku

  • Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, sun kai ziyartar jaje ga Rotimi Amaechi
  • Ziyarar da suka kai Port Harcourt ta biyo bayan rasuwar mahaifiyar Amaechi, inda aka shirya gudanar da jana’izar ta a karshen mako
  • Rahotanni sun nuna cewa tsofaffin gwamnoni Obi da Kwankwaso sun mika sakon ta’aziyyarsu ga Amaechi da iyalansa gabanin jana’izar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, sun je Port Harcourt domin jajanta wa tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Legit ta ruwaito cewa iyalan Amaechi sun sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Mary Amaechi, a ranar Alhamis, 16 ga Yuli, 2026, tana da shekaru 89.

Kara karanta wannan

Daga dawowa daga motsa jiki, sufatan ɗan sanda ya yi mutuwar fuju'a

Lokacin da 'yan NDC suka ziyarci Rotimi Amaechi
Rabiu Kwankwaso, Peter Obi da 'yan NDC a gidan Rotimi Amaechi a Rivers. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Legit Hausa ta tabbatar da ziyarar ne a wani sako da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na Facebook.

An tuna da Mary Amaechi a matsayin wadda ta shafe rayuwarta wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da hidima, yayin da ’yan Najeriya ke mayar da martani kan rasuwarta.

Yayin da ake shirin birne ta, ’yan siyasar biyu sun gana da Amaechi a ranar Juma’a, 4 ga Satumba, 2026, a gidansa da ke Port Harcourt.

Kamar yadda TVC ta ruwaito a X, tsofaffin gwamnonin Anambra da Kano sun mika sakon ta’aziyyarsu gare shi da sauran ’yan uwansa.

Manufar ziyara ga Amaechi

Obi, wanda aka tabbatar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na NDC a 2027, ya kai ziyarar ne tare da Kwankwaso, a wani mataki da masu lura da al’amura suka bayyana a matsayin nuna goyon baya ga Amaechi a lokacin da yake cikin alhini.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Amaechi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2027.

Abin da Kwankwaso ya ce

Bayan kammala ziyarar, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa sun kai wa tsohon gwamnan ziyara ne yayin da ake shirye-shiryen birne mahaifiyarsa.

Ya ce:

“Gabanin barina Port Harcourt, mun kai ziyarar jaje ga Mai Girma Rotimi Amaechi, dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC a Jihar Rivers.
“Mun mika sakon ta’aziyyarmu bisa rasuwar mahaifiyarsa gabanin gudanar da jana’izar ta.”

Legit ta wallafa cewa ziyarar jaje ta ja hankalin jama’a a kafafen sada zumunta. Wani mai amfani da shafin X, @chef_jenny25, ya yi tsokaci da cewa:

“Haka ya kamata a yi 👏👏”
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Mr Peter Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Mr Peter Obi a wajen taron NDC a Rivers
Source: Facebook

Gardadin Obi kan zaben 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa Peter Obi ya yi wata muhimmiyar sanarwa yayin wani taron tattaunawa da jama’a a Port Harcourt, Jihar Rivers, ranar Alhamis, gabanin zaben 2027.

Dan takarar shugaban kasa na NDC ya yi magana kan matsalolin IReV da suka janyo ce-ce-ku-ce bayan babban zaben shugaban kasa na 2023 da magudin zabe.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, shi ma ya yi wa magoya bayansa jawabi, inda ya gargadi ’yan Najeriya da kada su sake maimaita kura-kuran zabe na baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng