2027: Yadda Abba Kabir zai Kafa Tubalin Goyon Bayan Tinubu a Kano a Yau
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai halarci taron kaddamar da kungiyar magoya bayan Shugaba Bola Tinubu a Kano tare da tarbar sabbin ’yan jam’iyya
- Rahoto ya nuna cewa za a gudanar da taron ne a gobe Asabar, 5 ga Satumba 2026, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, a jihar Kano
- Taron zai kuma kasance wajen karbar wasu manyan ’yan siyasa da magoya bayansu da suka sauya sheka daga jam’iyyu daban-daban zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai halarci taron kaddamar da shugabancin kungiyoyin magoya bayan Shugaba Bola Tinubu a jihar Kano.
Za a gudanar da taron ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, inda kuma APC za ta karbi sababbin ’yan jam’iyya da suka sauya sheka daga wasu jam’iyyun siyasa.

Source: Facebook
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook ta bayyana taron a matsayin wani bangare na karfafa tsarin jam’iyyar APC a Kano.
Wadanda za a karba a APC
Daga cikin manyan ’yan siyasar da ake sa ran za a karba zuwa APC akwai Sanata Rufa’i Sani Hanga da mutanensa.
Haka kuma, ana sa ran Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da magoya bayansa za su halarci taron tare da tabbatar da shigar su jam’iyyar APC.
Sauran waɗanda aka bayyana sun haɗa da jagoran NNPP, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, da Mataimakin Shugaban NDC na jihar Hon. Ali Datti Yako tare da sauran shugabannin jam’iyyar.
Sauran da za a karba
Jerin waɗanda ake sa ran za su sauya sheƙa ya haɗa da Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Ungogo Hon. Badaru Umar, tare da tawagar gidan Gawuna.
Tsohon Shugaban Sajalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Isyaku Ali Danja da mutanensa na ɗaya daga cikin waɗanda za su shiga APC.
Haka kuma, Tsohon Mataimakin Ɗan Takarar Gwamna na PDP Hon. Yusuf Bello Danbatta da mutanensa za su kasance cikin waɗanda ake sa ran za a karba.

Source: Facebook
Sauran sun haɗa da Tsohuwar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman Sanata Baraka Sani, da Shugaban NNPP Hon. Abdullahi Zubairu Abiya.
Har ila yau, Tsohon Ɗan Takarar Sanata a NNPP Sanata Abdulmajid Dauda Dandawaki, da Ɗan Takarar Majalisar Jiha a Ƙarƙashin NDC Hon. Kabiru Adamu Kofar Ruwa na daga cikin waɗanda aka ambata.
Maganar Jibrin Kofa kan APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce APC ba za ta bar wa jam’iyyun adawa ko kujera daya daga cikin kujerun zabe a Kano a 2027 ba.
Kofa, wanda aka fi sani da Jarman Bebeji, ya bayyana hakan ne a Kofa yayin wata ganawa ta musamman da shugabannin APC da wakilan rumfunan zabe daga kananan hukumomin Kiru da Bebeji.
Ya ce yana da yakinin APC za ta ci gaba da rike shugabancin Najeriya tare da lashe dukkan kujerun zabe da ake da su a Kano a babban zaben 2027.
Asali: Legit.ng
