'Yan Bindiga Sun Addabi Kano, Abba Ya Fadi Matakan da za a Dauka a Murkushe Su

'Yan Bindiga Sun Addabi Kano, Abba Ya Fadi Matakan da za a Dauka a Murkushe Su

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da hare-haren 'yan bindiga da aka kai a kananan hukumomi hudu na jihar
  • Gwamnan ya ce gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace tare da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma
  • Ya bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa su kwantar da hankula tare da bai wa jami'an tsaro bayanan da za su taimaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamna, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da hare-haren 'yan bindiga da aka kai a wasu kananan hukumomin jihar, inda ya ce gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa gwamnoni umarni su inganta rayuwar talaka

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a ofis. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wuraren da aka kai hare-hare

Sanarwar da ya wallafa a Facebook ta ce yankunan da hare-haren suka shafa sun hada da Chiromawa da ke karamar hukumar Garun Malam, Beli a Rogo, Bebeji da kuma wasu al'ummomi da ke kusa da Gwarzo.

Gwamnan ya bayyana hare-haren a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba, tare da mika sakon ta'aziyya ga wadanda lamarin ya shafa da iyalan mutanen da abin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Najeriya da ya samu ribar Naira miliyan 10 a sayar da kosai

Matakan da za a dauka a Kano

Gwamnan ya tabbatar wa al'ummomin da abin ya shafa cewa gwamnatin jihar za ta dauki dukkan matakan da suka dace tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin hana sake aukuwar hare-hare da dawo da kwarin gwiwar jama'a.

Ya ce an umarci hukumomin da abin ya shafa da su karfafa sa ido, tattara bayanan sirri da kuma hanyoyin daukar matakin gaggawa a yankunan da lamarin ya shafa.

Daily Trust ta wallafa cewa Abba Kabir ya bukaci jami'an tsaro da su ci gaba da gudanar da ayyukan da suka dogara da bayanan sirri domin kare al'ummomin da ke cikin hadari a fadin jihar.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Kira ga jama'ar Kano

Gwamnan ya bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa su kwantar da hankula tare da kauce wa duk wani mataki da zai kara haddasa tashin hankali.

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

Ya kuma yi kira ga jama'a da su ba jami'an tsaro hadin kai tare da samar musu da sahihan bayanai da za su taimaka wajen dakile hare-haren da kuma cafke wadanda suka aikata su.

Gwamna Yusuf ya yaba wa jami'an tsaro bisa kokarin da suke yi, tare da bukatar su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro na musamman domin kare al'ummomin da ke cikin hadari.

Ya yi addu'ar Allah Ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu, Ya ba wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, sannan Ya dawo da mutanen da aka sace lafiya.

An sace shugaban APC a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Rogo a Kano, Abdullahi Alhassan Beli.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun shiga garin Beli da misalin karfe 10:30 na dare ranar Litinin, inda suka rika harbe-harbe kafin su nufi gidan shugaban jam'iyyar.

Wani kansila mai wakiltar Beli, Yakubu Bala, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce mazauna yankin da jami'an tsaro sun yi kokarin fatattakar maharan, amma ba su samu nasarar kama su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng