Ma’aikata Sun Yanke Sabon Mafi Karin Albashin da Suke So da N70, 000 Ta Yi Kadan

Ma’aikata Sun Yanke Sabon Mafi Karin Albashin da Suke So da N70, 000 Ta Yi Kadan

  • Kungiyar FWF ta mika bukatar karin albashin zuwa ga Shugaba Bola Tinubu, alkalin alkalai da Majalisar Tarayya a Najeriya
  • Shugabannin FWF sun ce albashin ₦70,000 ba ya isa saboda faduwar darajar kudi da tsadar kayayyaki da ake fama da su
  • An nemi a gyara albashin ma'aikata da ke mataki na 17 zuwa ₦1.5m don dacewa da halin da tattalin arzikin kasar yake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Wata kungiyar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta rubuta wa shugaba Bola Ahmed Tinubu da majalisa takarda a kara albashi.

Kungiyar tana son ganin mafi karancin albashin ma’aikacin gwamnatin tarayya ya tashi daga N70, 000 zuwa akalla N300, 000 yanzu.

Ma'aikata
Wasu ma'aikata a ranar da aka ware dominsu a Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wasikar FWF ta nemi a kara albashi

Punch ta ce shugaban kungiyar FWF na kasa, Andrew Emelieze da sakatarensa,Ogundele Ayodele suka rubuta wannan wasika.

An aika wasikar neman karin ga shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilan tarayya da kuma alkalin alkalai na Najeriya.

Kara karanta wannan

Shirin cire Tinubu a mulki: Jam'iyyar PDP ta fadi matsayarta kan hadaka a 2027

Haka kuma an aika wasilar zuwa ga shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya da Mai girma shugaban kasa wato Mai girma Bola Tinubu.

Ana so a rika biyan N300, 000 zuwa N1.5m

FWF ta kawo shawarar a rika biyan albashin N1.5m a kowane wata ga ma’aikatan da suka kai matakin aiki na 17 a gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta ce albashin da ake biya ba zai iya rika ma’aikata ba a yanzu sakamakon kalubalen tattalin arziki da ake fuskata a kasar.

Andrew Emelieze da Ogundele Ayodele suna so albashin mafi karancin albashin ma'aikaci ya zama N300, 000 sai N1.5m ya zama mafi yawa.

Ina karin albashin da aka yi a 2024?

Duk da karin da aka yi wa ma’aikata a 2024, kungiyar ta ce har gobe wasu ma’aikatan ba su gama karbar hakkokinsu da wasu alawus ba.

Ma’aikatan sun ce abin da aka yi wa ma’aikata a shekarar 2024 da aka yi karin albashi kawai shi ne kowa ya samu karin N40, 000 a wata.

The Guardian ta rahoto su suna cewa ma’aikatan gwamnati su ne kashin bayan harkokin tattalin arziki don haka sun cancanci kari.

Kara karanta wannan

Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

Halin da ma'aikata suke ciki a yau

Duk da doka ta yi tanadin sai bayan shekaru uku za a duba albashi, FWF ta ce wannan bai kamata ya hana a duba halin da ake ciki ba.

Shugabannin na FWF sun ce kasada ce ma’aikata su cigaba da zuwa ofis a wannan yanayi.

Wasikar ta yi bayanin yadda bashi ya yi wa ma’aikata katutu domin sai sun karbi aro za su yi zuwa ofis ban da sauran dawainiyar rayuwa.

Ma'aikata
Ma’aikatan gidan jarida a wani kamfani a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda FWF take so a maida albashi

Level 1 - N300, 000

Level 2 - N330,000

Level 3 - N360,000

Level 4 - N390,000

Level 5 - N420,000

Level 6- N450,000

Level 7 - N480,000

Level 8 - N510,000 -

Level 9 - N550,000

Level 10 - N600,000

Level 12 - N700,000

Level 13 - N750,000

Level 14 - N800,000

Level 15 - N1m

Level 16 - N1.2m

Level 17- N1.5m

Gwamnati ta yi sojoji karin albashi

Kara karanta wannan

Yadda ake ciki a kasar Nijar da sojoji suka yi yunkurin yi wa Tchian juyin mulki

An ji Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsarin albashi ga sojoji kusan 250,000 wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2026.

Sabon tsarin ya kawo ƙarin albashi tsakanin 30% zuwa 80%, inda ƙaramin soja (Private) zai koma karɓar ₦187,200 maimakon ₦104,000.

Wannan ƙari zai sa kasafin albashin sojojin da gwamnatin tarayya ke fitarwa ya ƙaru daga ₦660bn zuwa ₦924bn a kowace shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng