Yadda aka Samo Kalmar Takutaha da Fara Bikin a Najeriya
- A wasu biranen ƙasar Hausa, musamman Kano, ana gudanar da bikin Takutaha ne a rana ta bakwai bayan ranar Maulidin Annabi Muhammad (SAW)
- Bikin ya zama wani muhimmin ɓangare na al’adar Hausawa, inda ake gudanar da shagulgula, dafe-dafe, yanka da sauran bukukuwa domin murna
- Masanin harshen Hausa da al’adun Hausawa, Dr Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible), ya bayyana cewa kalmar Takutaha tana da alaƙa da Hausa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – A wasu biranen ƙasar Hausa, musamman jihar Kano, bikin Takutaha na daga cikin bukukuwan da ake gudanarwa bayan zagayowar ranar Maulidin Annabi Muhammad (SAW).
Ana gudanar da bikin ne a rana ta bakwai daga ranar Maulidi, wadda ta yi daidai da ranar da Hausawa suka saba gudanar da bikin suna ga jaririn da aka haifa.

Source: Facebook
Wani rahoto da BBC Hausa ta wallafa ya nuna cewa ranar bakwai da haihuwa ne aka saba yin raɗa suna, yanka da kuma taron biki idan aka samu ƙaruwa.
Ranar yin Takutaha
Domin gano asalin kalmar Takutaha, an tuntubi tsohon Kwamishinan Addini na jihar Kano kuma masanin harsunan Najeriya da al’adun Hausawa, Dakta Muhammad Tahar Adam, wanda aka fi sani da Baba Impossible.
Baba Impossible ya ce bikin ana gudanar da shi ne a rana ta bakwai bayan zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammad (SAW).
Ya bayyana cewa Annabi Muhammad (SAW) an haife shi ne a ranar 12 ga wata, kuma idan ranar ta zagayo, ana gudanar da bikin suna a rana ta bakwai, wadda ake kira ranar Takutaha.
Asalin kalmar Takutaha
Baba Impossible ya bayyana cewa asalin sunan Takutaha yana da alaƙa da wani lamari da ya faru a zamanin Shehu Usman Ɗanfodio.
Ya ce a lokacin da mutane suka fito cikin gari suna zagayawa suna murnar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), Shehu Ɗanfodio ya fito ya tambaye su abin da ke faruwa.
Ya ce mutanen sun amsa masa cewa suna murnar ranar sunan Annabi. Baba Impossible ya ce a lokacin ne Ɗanfodio ya ce, “Ku tai, taku ta”, ma’ana su tafi, domin wannan taku ce.
Ya bayyana cewa daga wannan furuci ne kalmar “Takutaha” ta samo asali, inda daga baya ta zama sunan bikin da ake gudanarwa a ranar bakwai bayan Maulidi.
A yanzu bikin Takutaha ya bazu zuwa wasu jihohin da ba a saba gudanar da shi a baya ba, ciki har da jihar Gombe da wasu sassan Arewacin Najeriya.

Source: Original
Maganar Abba kan Takutaha
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bukaci Musulman jihar da su yi amfani da bikin Takutaha wajen tuna Annabi Muhammad (SAW).
Gwamnan ya jaddada muhimmancin zaman lafiya, tausayi, adalci da haƙuri, yana mai cewa waɗannan kyawawan halaye ya kamata su kasance cikin rayuwar Musulmi a kullum.
Ya ce Takutaha wani muhimmin ɓangare ne na tarihin Kano, wanda tsawon shekaru ya kasance wata hanya ta haɗa kan al’ummar jihar.
Asali: Legit.ng

