Bayan Caccakar Atiku kan Tallafi, za a Rage Kudin Fetur a Najeriya
- Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta ce gidajen mai da ke Abuja za su fara rage farashin man fetur a famfunansu cikin ‘yan kwanaki masu zuwa
- Kakakin IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce dillalan na shirin sauya farashin da dabarun sayar da fetur da zarar sababbin kayayyakin sun fara shiga kasuwa
- Ya ce zuwan kayayyakin zai iya kawo sauye-sauye a kasuwar man fetur, yayin da ake sa ran rage farashin zai ba masu amfani damar ci gaba da saye da sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta ce gidajen mai da ke Babban Birnin Tarayya (FCT) za su fara rage farashin man fetur a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Rahotanni sun nuna cewa sakatare janar na yaɗa labarai na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya bayyana hakan ne yayin wata hira.

Source: Getty Images
Farashin mai zai sauka
Vanguard ta wallafa cewa Ukadike ya ce dillalan man fetur na shirin sauya farashinsu da dabarun sayar da kayayyaki da zarar sababbin kayayyakin sun fara shiga kasuwa.
Ya ce zuwan sababbin kayayyakin na iya kawo sauye-sauye a kasuwar man fetur, musamman yadda gidajen mai za su daidaita farashin da suke sayarwa.
Daily Nigerian ta walllafa cewa ya ce dillalan za su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa masu amfani sun ci gaba da samun kayayyakin da suke bukata.
Yaushe fetur zai sauka?
Sai dai Ukadike ya ce har yanzu ba a san takamaiman ranar da sababbin kayayyakin za su fara shigowa kasuwa ba, saboda dillalan ba su samu tabbatacciyar ranar fara tsarin ba.
Ya ce duk wani matakin da za a dauka zai kasance ne bisa dokoki da ka’idojin da ake da su a fannin sayar da man fetur.
“Da zarar sabbin kayayyakin sun fara shigowa, ana sa ran dillalai za su gaggauta duba farashinsu tare da sabunta kayayyakin da suke bayarwa.
“Bayan wannan tsari, idan muka fara saye gobe ko jibi, da zarar an fara, za mu daidaita farashinmu kuma mu fara samar da sababbin kayayyakin ga jama'a.
“Sayen kayayyakin na iya farawa cikin ‘yan kwanaki, gwargwadon lokacin da aka fara aiwatar da tsarin a hukumance,”
In ji shi.

Source: Getty Images
Farashin Dangote a Abuja
Rahotanni sun nuna cewa matatar man fetur ta Dangote ta ƙara farashin man da ake ɗauka daga ma’ajiyarta, daga N1,165 zuwa N1,185 kan lita.
Daga bisani, farashin ya sake tashi zuwa N1,200 sannan ya kai N1,265 cikin makon da ya gabata. An ce ƙarin farashin ya riga ya bayyana a farashin da ake sayar da fetur a gidajen mai daban-daban da ke Abuja.
Dangote ya faɗaɗa raba fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa matatar Dangote ta faɗaɗa shirin kai kayayyakin man fetur kyauta zuwa jihohin Kano, Imo, Anambra da Nasarawa.
Ana sa ran matakin zai rage kudin da dillalan man fetur masu zaman kansu ke kashewa wajen jigilar kayayyaki, tare da samar da damar rage farashin fetur ga masu saye.
Shirin, wanda ya fara da kai kayayyakin zuwa Legas, Ogun, Rivers, Kaduna, Delta da Abuja, na nufin kusantar da kayayyakin man fetur ga dillalai da masu sayarwa tare da rage kudin jigila.
Asali: Legit.ng

