Da Gaske Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ya Fice daga Jamiyyar APC? An Gano Gaskiya
- Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya fice daga APC
- Binciken gano gaskiya da aka yi ya nuna cewa Akpabio yana karanta wasikar murabus din wani dan majalisa ne, ba tasa ba
- An tabbatar da cewa Sanata Olubiyi Fadeyi Ajagunla ne ya bar APC ya koma PDP, ba Godswill Akpabio ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta yana ikirarin cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya sanar da murabus daga jam'iyyar All APC.
Akpabio shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya ta 10 da aka rantsar a shekarar 2023 kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki.

Source: Facebook
Wani shafin Facebook mai suna The Opposition ne ya wallafa bidiyon mai tsawon sakanni 18, inda aka ji Akpabio yana cewa:
“Ina rubuta wannan wasika domin gabatar da murabus dina daga APC a hukumance daga yau. Ban dauki wannan mataki cikin sauki ba…”
Bidiyon ya jawo martani daga masu amfani da Facebook, inda wasu suka yarda da ikirarin yayin da wasu suka nuna shakku kan sahihancinsa.
Abin da bincike ya gano
Jaridar Dubawa ta gudanar da bincike kan ikirarin saboda matsayin Akpabio a siyasar Najeriya da kuma yadda batun ya bayyana a lokacin da harkokin siyasa ke kara zafi gabanin babban zaben 2027.
Domin tabbatar da sahihancin bidiyon, ta dauki hoton wani bangare daga ciki tare da gudanar da binciken hoton ta hanyar amfani da tsarin reverse image search.
Binciken ya kai ga wani cikakken bidiyo mai tsawon mintuna bakwai da sakanni 44 da wani shafin Facebook mai suna Osogbo Updates ya wallafa.
Bayan nazarin cikakken bidiyon, an gano cewa Akpabio ba ya sanar da murabus dinsa daga APC ba ne.
Maimakon haka, yana karanta wasikar murabus ta Sanata Olubiyi Fadeyi Ajagunla, mai wakiltar mazabar Osun ta Tsakiya a majalisar dattawa.
Wane ne ya bar jam'iyyar APC?
Wasikar da Akpabio yake karantawa ta sanar da majalisar dattawa cewa Fadeyi Ajagunla ya yi murabus daga jam'iyyar APC tare da sauya sheka zuwa PDP a watan Yulin 2026.
An kuma binciki shafukan sada zumunta na APC, majalisar dattawan Najeriya da kuma Sanata Godswill Akpabio domin gano ko akwai wata sanarwa kan murabus dinsa daga jam'iyyar.
Sai dai ba a samu wata sanarwa makamanciyar haka ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.

Source: Twitter
Da gaske Akabio ya fice daga APC?
Ikirarin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da murabus daga APC ba gaskiya ba ne.
Binciken Dubawa ya nuna cewa an yanke bidiyon tare da sauya mahallinsa domin ya sa mutane su yi tunanin Akpabio ne yake sanar da murabus dinsa.
A hakikanin gaskiya, Akpabio yana karanta wasikar murabus ta wani dan majalisar dattawa ne a yayin zama. Olubiyi Fadeyi Ajagunla ne ya bar APC ya koma PDP, ba Godswill Akpabio ba.
Tinubu ya gana da Sanata Alpabio
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa ba a bayyana batun da shugabannin biyu suka tattauna a kansu ba yayin da ake shirin tunkarar babban zaben 2027.
Asali: Legit.ng


