‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Janar, Sojoji Sun Bi Daji sai da Suka Ceto Ta

‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Janar, Sojoji Sun Bi Daji sai da Suka Ceto Ta

  • Sojojin Najeriya sun ceto Mrs Adonkie lami lafiya a kauyen Angwan Sabo bayan jin labari masu garkuwa sun yi gaba da ita
  • An cafke mutane biyu daga cikin tawagar masu garkuwa da mutanen a kusa da kauyen Gaube da ke yankin Kuje a Abuja
  • Sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da alburusai guda daga hannun wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa dakarunsu sun ceto matar wani tsohon janar da aka dauke ta a babban birnin Abuja.

Ana fama da matsalar tsaro sosai musamman a Arewacin Najeriya, wannan karo abin ya shiga gidan janar na soja har cikin Abuja.

Motar sojoji
Wasu motocin yakin sojoji a Maiduguri lokacin fadan Boko Haram Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Jawabi daga hedikwatar sojojin kasa

A wani jawabi da hedikwatar sojojin kasa ta fitar a kafar Facebook, an ji cewa an yi nasarar ceto mai dakin Janar Basil Adonkie.

Misis Adonkie Basil Adonkie ta shaki iskar ‘yanci a ranar Talata 1 ga Satumba 2026 a wani kokari na hadin guiwar dakarun kasa.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kutsa cikin daji, sun kubutar da matasan NYSC da aka yi garkuwa da su

Sanarwar da aka fitar daga gidan sojan ta bayyana cewa bayanan sirri ne suka zo masu har aka yi nasarar kubutar da ita.

Sojojin kasa sun sa 'yan bindiga shiga jeji

Da aka yi artabu da ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da matar, a karshe dole suka tsere zuwa jeji saboda barin wutan sojoji.

Ba girma babu arziki ‘yan bindigan suka hakura da matar da suka dauka, daga nan sojoji suka dauk ta a kauyen Angwan Sabo.

“Bayan samun ingantattun bayanan sirri, sai dakaru suka ratsa yankin Aco Estate–Goza kuma suka cin ma masu garkuwa da mutanen.
Da sojoji suka fi karfinsu wajen luguden wuta a harin gaggawan da suka kai, miyagun sun jefar da wanda suka kama sannan suka tsere zuwa jejejin da ke kusa, a sanadiyyar haka aka yi nasarar ceto Misis Adonkie a kauyen Angwan Sabo.

- Hedikwatar sojojin kasa

An rufe hanya saboda neman 'yan bindiga

Sanarwar ta ce sojojin sun kuma kutsa cikin shiyyar Aco Estate–Angwan Sayawa yayin da aka baza wasu dakarun su toshe hanya.

Kara karanta wannan

Yadda ake ciki a kasar Nijar da sojoji suka yi yunkurin yi wa Tchian juyin mulki

An rufe hanyoyin ne ko za a iya rutsa ‘yan bindigan, a hana su tserewa daga cikin jeji, wannan labari ya fito a jaridar The Cable dazu.

A irin wannan kokari ne a ranar 2 ga Satumba 2026 dakarun sojoji suka yi ram da wani gungun ‘yan bindiga a kauyen Gaube a Kuje.

Sojojin da ke fadar shugaban kasa da wasu a hedikwata sun kama mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Kuje.

Sojojin sun same su da bindigar Ak-47 da casbi 19 na harsashi mai tsawon 7.62mm kamar yadda aka tabbatar a hotuna da aka saki.

Yanzu dai bayanai sun ce ana cigaba da lalube a yankin da nufin kama ragowar wadanda ake zargi da laifin yin garkuwa da mutane a jeji.

Sojoji sun hana juyin mulki a Nijar

An ji labari Sojojin Jamhuriyar kasar Nijar sun dakile yunkurin juyin mulki a birnin Niamey, inda gwamnatin sojan ke ci gaba da rike iko.

Jami'an tsaron kasashen Nijar da dakarun Rasha sun samu nasarar murkushe yunkurin juyin mulkin da wasu sojojin tawaye suka nemi yi.

Kara karanta wannan

Ta faru ta ƙare: Sojoji sun shiga maɓoyar ƙasurgumin ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu

An nemi a kifar da Shugaba Abdourahamane Tchiani amma gwamnati ta tabbatar da shawo kan boren sannan abubuwa sun dawo daidai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng