Gado ba Karambani ba: Dan Ministan Tinubu Mai Shekaru 28 Ya Lashe Zaben Ciyaman
- Osborn Nweze Umahi, ɗan Ministan Ayyuka David Umahi mai shekaru 28, ya zama zababben shugaban ƙaramar hukuma
- Umahi ya yi takarar kujerar shugaban Ohaozara ƙarƙashin APC, inda ya yi alkawarin fifita gaskiya, ingantaccen aiki da samar da ci gaba
- Bayan nasararsa, Umahi ya sha alwashin barin albashi da alawus ɗinsa gaba ɗaya, tare da mai da hankali kan ci gaban matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abakaliki, Ebonyi - Dan Ministan Ayyuka David Umahi, Osborn Nweze Umahi ya fafata a zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Ebonyi.
Matashin mai shekaru 28, ya zama zababben shugaban ƙaramar hukumar Ohaozara a Ebonyi a zaben da aka yi.

Source: Facebook
Dan tsohon gwamnan Ebonyi ya zama ciyaman
Ya samu nasarar ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar, inda ya tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar APC, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027
A lokacin kamfen, Umahi ya yi alkawarin gudanar da mulki bisa gaskiya da riƙon amana, inganta ayyukan jama’a da samar da sakamako mai ma’ana.
Jim kaɗan bayan bayyana nasararsa, shugaban da aka zaɓa ya yi alkawarin cewa ba zai karɓi albashi ko alawus ɗinsa ba a tsawon wa’adinsa.
Ya ce matakin na nufin nuna cewa burinsa na neman mukamin ba don tara dukiya ko amfanin kansa ba ne, illa hidima ga al’umma.

Source: Original
Alkawarin dan tsohon gwamnan Ebonyi a kamfen
Umahi ya kuma yi alkawarin ba da fifiko ga bunƙasa ababen more rayuwa, ƙarfafa tattalin arziki da samar da shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar jama’a.
Ya ce zai kuma mai da hankali kan shirye-shiryen da suka shafi matasa domin samar musu da damammaki da inganta rayuwarsu a Ohaozara.
Umahi injiniya ne kuma ɗan kasuwa, sannan shi ne ɗan David Umahi, Ministan Ayyuka na Najeriya kuma tsohon gwamnan Ebonyi.
Tasirin da ake ganin Osborn zai yi

Kara karanta wannan
2027: ADC ta fito da bayani, an ji dalilin Atiku na ƙin sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya
Nasarar da Umahi ya samu yana da shekaru 28 ana sa ran za ta ƙara haifar da muhawara kan sauyin ƙarni a siyasar Najeriya.
Haka kuma, lamarin na iya ƙara jawo hankali kan yadda matasa ƙwararru ke ƙara shiga harkokin siyasa da gudanar da ƙananan hukumomi a Najeriya.
Sai dai ga mazauna Ohaozara, abin da zai fi muhimmanci yanzu shi ne yadda Umahi zai sauya alkawuran kamfen zuwa ayyukan ci gaba na zahiri.
Za su kuma sa ido kan yadda zai aiwatar da shirye-shiryensa tare da inganta ababen more rayuwa da samar da damammaki ga al’ummar ƙaramar hukumar.
Umahi ya fadi alherin Tinubu
A baya, an ji cewa Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana ayyukan alheri da shugaba Bola Tinubu ke yi a fadin Najeriya wanda ya cancanci tazarce.
Umahi ya ce gwamnatin Tinubu na mai da hankali kan inganta ababen more rayuwa a yankin, musamman manyan tituna.
Ministan ya danganta rawar da yake takawa da samun ayyukan raya kasa ga yankin, yana cewa Ubangiji ne ya turo shi ya faɗi gaskiya.
Asali: Legit.ng