2027: An Yi Hasashen Jihar Kaduna da Sauran Wasu 8 da Atiku Zai Lashe a Zaɓe

2027: An Yi Hasashen Jihar Kaduna da Sauran Wasu 8 da Atiku Zai Lashe a Zaɓe

  • Kungiyar Political Intelligence Group ta yi hasashen yawan jihohin da Atiku Abubakar zai lashe a zaɓen 2027
  • Hasashen ya nuna Atiku zai samu nasara a jihohi da dama daga Arewacin Najeriya yayin Peter Obi zai lashe jihohi takwas
  • Kungiyar ta ce hasashen ya dogara ne kan halin siyasar yanzu, kuma sauye-sauyen tattalin arziki, hadaka na iya sauya sakamakon kafin 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar Political Intelligence Group (PIG) ta fitar da wani hasashe da ke nuna cewa Atiku Abubakar zai iya lashe jihohi tara a zaben shugaban kasa na 2027.

An bayyana wannan hasashe ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shekarar 2027 a Najeriya.

An yi hasashen jihohin da Atiku zai lashe
Yan takarar shugaban kasa a jam'iyyun ADC, Atiku Abubakar, NDC, Peter Obi da na APC, Bola Tinubu. Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Legit.ng ta ruwaito cewa hasashen, wanda aka wallafa a Politico.ng, ya dogara ne kan yanayin siyasar Najeriya kamar yadda yake ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

Kano da wasu jihohi 19 sun fito a wuraren da Bola Tinubu zai samu nasara a zaben 2027

Yadda aka yi hasashen zaben 2027

PIG ta tantance yadda goyon bayan al’umma yake tsakanin manyan ‘yan takarar shugaban kasa uku, inda ta sanya Atiku na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayi na biyu.

Kungiyar ta yi hasashen cewa Atiku zai lashe jihohi tara, yayin da Peter Obi na Nigeria Democratic Congress (NDC) zai samu nasara a jihohi takwas.

Sai dai PIG ta bayyana cewa hasashen ba shi ne sakamakon karshe na zaben ba, domin yanayin siyasa na iya sauyawa sosai kafin ranar kada kuri’a.

Karfin Tinubu da Atiku a Najeriya

A karkashin hasashen PIG, Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da karfin gaske a Kudu maso Yamma, sannan yana samun nasara a wasu jihohin wajen yankinsa.

Wannan ya ba shi damar samun adadi mafi yawa idan aka kwatanta da sauran ‘yan takarar. PIG ta yi hasashen cewa Tinubu zai lashe jihohi 20.

A bangaren Atiku kuwa, kungiyar ta ce zai yi karfi musamman a Arewacin Najeriya, inda Kaduna da wasu jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma suke cikin jerin wuraren nasararsa.

Kara karanta wannan

Shirin cire Tinubu a mulki: Jam'iyyar PDP ta fadi matsayarta kan hadaka a 2027

Jihohin da PIG ta yi hasashen Atiku zai lashe sun hada da Sokoto, Kebbi, Niger, Katsina, Kaduna, Jigawa, Gombe, Adamawa da Taraba.

PIG ta danganta karfin Atiku a Arewa da dimbin hanyoyin sadarwarsa na siyasa da kuma gogewarsa wajen yakin neman zaben shugaban kasa a baya.

An yi hasashen jihohi 9 da Atiku zai ci a 2027
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Abubuwan da za su iya sauya hasashen

PIG ta jaddada cewa bai kamata a dauki wannan hasashe a matsayin sakamakon karshe na zaben 2027 ba, cewar Daily Post.

Zaben yana nan gaba, don haka akwai isasshen lokaci da yanayin siyasa zai iya sauyawa kafin ‘yan Najeriya su kada kuri’unsu.

Tattalin arzikin kasa na iya inganta ko tabarbarewa, sabbin kawance na siyasa na iya samuwa, yayin da shaharar ‘yan takara kuma za ta iya karuwa ko raguwa.

Tinubu zai iya kare manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa, yayin da matsayin Atiku kan tallafin man fetur zai iya zama muhimmin batu a yakin neman zabe.

A halin yanzu, hasashen PIG ya sanya Tinubu a gaba da jihohi 20, Atiku na biyu da jihohi tara, sannan Obi na uku da jihohi takwas.

Kara karanta wannan

INEC ta fitar da sunayen yan takarar gwamna na jihohi a zaben 2027, an canza wasu

Atiku ya yi alkawari kan kananan hukumomi

Mun ba ku labarin cewa Atiku Abubakar ya ce zai tabbatar da biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye idan ya zama shugaban Najeriya.

an takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC ya ce gwamnatinsa za ta mutunta hukuncin kotu tare da kare cin gashin kan ƙananan hukumomin Najeriya.

tiku ya zargi gwamnatin Tinubu da jinkirta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan ‘yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.