Babbar Magana: Amurka da Isra'ila na Yunkurin Hada Wasu Kasashen Musulmi Fada da Juna
- Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya zargi Isra’ila da Amurka da ƙoƙarin haɗa fada tsakaninnƙasashen Musulmi domin mallakar arzikin yankin
- Pezeshkian ya ba da misali da yadda Amurka ta kai wa Iran hari ta hanyar amfani da sararin samaniyar wasu ƙasashen Musulmi
- Ya ce Iran za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka yayin da yake bayyana takunkuman Amurka a matsayin kuskuren lissafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Shugaban kasar musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce Isra’ila da Amurka suna ƙoƙarin haɗa ƙasashen Musulmi faɗa da juna domin su samu damar sarrafa arzikin yankin.
Shugaba Pezeshkian ya yi wannan zargin ne yayin ake ci gaba da musayar wuta da nuna wa juna yatsa tsakanin kasar Iran da Amurka da Isra'ila.

Source: Getty Images
Masoud Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata hira da Al Jazeera, inda ya ce Isra’ila da Amurka sun kai wa Iran hare-hare “ta sararin samaniyar ƙasashen Musulmi”.
Ya ce “maƙiya” na ƙoƙarin tayar da rikici tsakanin jami’an gwamnatin Iran, amma ya ƙara da cewa “a yau Iran na ganin haɗin kai da haɗin gwiwa da ba a taɓa ganin irinsa ba”.
Kasar Iran za ta tsaya tsayin daka
Pezeshkian ya ce Iran za ta ci gaba da “tsayawa tsayin daka” wajen fuskantar Amurka da Isra’ila, duk da takunkuman da ya bayyana a matsayin “kuskuren lissafi”.
Shugaban na Iran ya ce waɗanda suka yi tunanin za su iya cutar da al’ummar kasar Musulunci ta Iran ta hanyar kakaba musu takunkumi sun yi kuskuren lissafi.
Pezeshkian ya ce Amurka da Isra’ila na ƙoƙarin “hana Iran dogaro da kanta”, amma Iran za ta mayar da hankali wajen saka hannun jari a cikin al’ummarta, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Iran ta zargi Amurka da tada rikici
Ya kuma ce Amurka da Isra’ila sun “jawo” ƙasashen yankin cikin yaƙi, suna tunanin cewa gwamnatin Iran “za ta faɗi cikin kwanaki kadan”.
Sai dai ya ce duk da hakan, ’yan Iran sun “tsaya tsayin daka a gaban hare-haren Amurka da Isra’ila, kuma za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka don kare kansu”.

Source: Getty Images
Ya ƙara da cewa za a iya samun tsaron yankin ne ta hanyar “haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin”, yana mai cewa yankin ba ya buƙatar “ɗan sanda” da zai riƙa kula da shi.
Trump ya yi fatali da tayin Iran
A wani labarin, kun ji cewa Iran ta gabatar da wani tsari ga Amurka na sake buɗe mashigar Hormuz mai matuƙar muhimmanci, amma cikin sa’o’i kaɗan rahotanni suka bayyana cewa Shugaba Donald Trump ya yi watsi da shirin.
Rahoton ya ce shugaban mai shekaru 80 na shakkar cewa Tehran za ta cika buƙatunsa, sannan ya ƙara da cewa Trump na ganin yiwuwar sake kai hare-haren bama-bamai.
Asali: Legit.ng

