An Gano Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi da Zai Iya Sa Tinubu Faduwa a Zaben 2027

An Gano Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi da Zai Iya Sa Tinubu Faduwa a Zaben 2027

  • Ogundamisi ya ce Tinubu ƙwararren ɗan siyasa ne, kuma ya gina ƙaƙƙarfan haɗaka da gwamnoni da manyan ’yan siyasa daga yankuna daban-daban
  • Ya ce duk da ƙarfin Tinubu a tsakanin ’yan siyasa, shugaban ya gaza gina haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin gwamnatinsa da talakawan Najeriya
  • Tsohon sakataren OPC ya ce Peter Obi ya fi dacewa ya zama babban abokin hamayyar Tinubu, yana kuma kira ga Atiku ya janye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon sakataren kungiyar Odua Peoples Congress (OPC), Kayode Ogundamisi, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Kayode Ogundamisi ya ce ƙaƙƙarfan haɗin kan siyasar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ka iya kasa tabbatar masa da nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, idan 'yan Najeriya suka hada kai.

Kayode Ogundamisi ya ba 'yan Najeriya shawara kan Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Ogundamisi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Rudolf Okonkwo a shirin 90Minutes Africa, inda ya yi nazari kan yanayin siyasar Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya bayyana mutanen da za su taka muhimmiyar rawa a tazarcen Tinubu

Ya ce Tinubu ya nuna ƙwarewa sosai wajen harkokin siyasa, musamman bayan ya fahimci cewa goyon bayansa na raguwa a wasu sassan Arewa.

A cewarsa, shugaban ya mayar da hankali wajen sake gina haɗin gwiwar siyasa da ya haɗa da yankin Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Kudu, wasu sassan Kudu maso Gabas da Arewa maso Gabas.

“Shugaba Tinubu ƙwararren ɗan siyasa ne,” in ji Ogundamisi.

Ya yaba wa Tinubu kan dabarun siyasa

Tsohon sakataren OPC ya amince cewa Tinubu ya samu damar jawo gwamnoni da wasu manyan jiga-jigan siyasa zuwa wajensa, lamarin da ya nuna ƙarfin tsarin siyasarsa.

Ya ce idan aka yi la’akari da yadda shugaban ya samu damar haɗa manyan ’yan siyasa a bayansa, wasu za su iya ganin cewa ya riga ya shirya sosai domin tunkarar zaɓen 2027.

“Ya gina haɗin gwiwarsa tsakanin ’yan siyasa ta hanyar samun kusan dukkan gwamnoni,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗauki zafi, Bola Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin APC a Aso Rock

Sai dai Ogundamisi ya ce akwai babban gibi tsakanin haɗin kan ’yan siyasa da haɗin kan talakawan ƙasar.

“Amma ya gaza gina haɗin gwiwa tsakanin al’ummar Najeriya,” In ji shi.

Ya soki gwamnatin Tinubu kan cin hanci

Ogundamisi ya kuma yi zargin cewa matsalar cin hanci da rashawa a gwamnatocin dimokuraɗiyya na Najeriya ta kai wani matsayi mai matukar tayar da hankali.

Ya ce lamarin ya ƙara muni a ƙarƙashin gwamnatin yanzu, yana mai cewa gwamnati ta samar da wata sabuwar hanyar da ya kira “salon satar kuɗi na kimiyya.”

A cewarsa, kasancewar kasafin kuɗi da dama da ake tafiyarwa lokaci guda da kuma bullar wasu hukumomin gwamnati na bogi na daga cikin abubuwan da ke nuna yadda ake tafiyar da harkokin kuɗaɗen gwamnati.

Ogundamisi ya zaɓi Peter Obi

Da aka tambaye shi wanda yake ganin ya kamata ya zama babban ɗan takarar da zai ƙalubalanci Tinubu a 2027, Ogundamisi ya nuna goyon bayansa ga Peter Obi, ɗan takarar Nigeria Democratic Congress (NDC).

Ya ce Obi ya fi dacewa da halin da Najeriya ke ciki, musamman idan aka yi la’akari da yadda yake kallon matsalolin talakawa.

Kara karanta wannan

Tirkashi: APC ta dauka da zafi bayan Atiku ya yi wasu kalamai

“Idan ka ajiye Peter Obi da Shugaba Tinubu gefe da gefe ta fuskar tausayi, Peter Obi ya fi." in ji shi.

Ya ce Najeriya na buƙatar shugaban da zai nuna tausayi ga jama’a tare da mayar da hankali kan matsalolin da suke fuskanta.

Ya ce sakamakon zaɓen 2027 zai iya dogara ba kawai kan ƙarfin haɗin kan ’yan siyasa ba, har ma kan yadda ’yan Najeriya za su mayar da martani ga halin tattalin arziki da matsalolin rayuwar da suke fuskanta.

Ogundamisi ya yi magana kan Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya samu goyon baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin hukumomi, ma’aikatu da wasu hukumomin gwamnati da gwamnatin tarayya sun fara shirin goyon bayan Bola Tinubu.

Masu mukaman sun naɗa sun fara wani gangami na haɗin gwiwa domin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng