"Allah Ne Kadai Zai Iya Dakatar da Shi," Datti Ya Hango Abin da ke Shirin Faruwa a Zaben 2027

"Allah Ne Kadai Zai Iya Dakatar da Shi," Datti Ya Hango Abin da ke Shirin Faruwa a Zaben 2027

  • Datti Baba-Ahmed ya ce Allah ne kaɗai zai iya hana Shugaba Bola Tinubu lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na LP ya ce Tinubu ya shafe shekaru 16 yana gina tsarin siyasa
  • Ya ce Tinubu ya yi nasarar kafa ƙawance da wasu ‘yan siyasa tare da rinjayar kusan kowa a fagen siyasar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Datti Baba-Ahmed, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, ya ce Allah kaɗai zai iya hana Shugaba Bola Tinubu lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Datti ya ce bai yarda da manufofin Tinubu ba, amma ya amince da ƙwarewar shugaban wajen ƙulla ƙawancen siyasa da kuma tsara harkokin siyasa tsawon shekaru.

Datti.
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Dati Baba-Ahmed Hoto: Datti Baba-Ahmed
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Trust TV, inda ya yi magana kan yadda harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027 da kuma tarihin ’yan takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Atiku zai yi amfani da matasa miliyan 1.5 domin kare kuri'un ADC

Ya ce Tinubu ya shafe kusan shekaru 16 yana gina tsarin siyasa, sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen shigar da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari cikin ƙawance gabanin zaɓen 2015.

“Ko da yake ban amincewa da shi gaba ɗaya ba, smma ya yi abin da wasu ba su iya yi ba. Ya shafe shekaru 16 yana tsarawa, ba wai shiryawa kawai ba," in ji shi.

Ya kwatanta Tinubu da Atiku

Datti ya kwatanta hakan da tsarin Atiku Abubakar, inda ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasan na iya kasancewa bai iya bin irin wannan dabara ba saboda turjiya daga mutanen da ke kusa da shi.

Datti ya bayyana nasarar Tinubu a zaɓen 2023 a matsayin wata babbar nasarar siyasa da ba kasafai ake ganin irinta ba, yana cewa shugaban ya yi kamar wanda ya “ci caca mai lambobi 16”.

Haka kuma, Datti ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ke da gagarumin iko a fagen siyasar Najeriya, yana cewa shugaban ya “rinjayi kusan kowa”.

Kara karanta wannan

Shettima ya tafi muhimmin taron da za a yi da Iran, Rasha da wasu kasashe

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tinubu ya fi karfin yan adawa

Datti ya yi ikirarin cewa jam’iyyun adawa ba su da tsari, sannan ya nuna cewa Tinubu na da isasshen tasiri da zai hana sauran jam’iyyun siyasa haɗa kai domin kalubalantarsa.

A rahoton The Cable, ya kara da cewa:

“Shi (Tinubu) ba zai bari su (’yan adawa) su haɗu ba. Wataƙila ma shi ne yake zaɓar ’yan takara a jam’iyyun adawa. Shi ne yake kafa shugabanci a waɗannan jam’iyyun siyasa. Yana yin abubuwan da kai da ni ba za mu iya zato ba.
“Idan Tinubu ya ce wani abu zai faru, Allah Maɗaukaki ne kaɗai zai iya hana faruwar sa. Idan ya ce za a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a 2027, Allah Maɗaukaki ne kaɗai zai iya hana hakan."

"Tinubu bai fi karfin a kayar da shi ba"

Kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na APM, Lawal Daura, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai fi karfin a kayar da shi a zaben shugaban kasa na 2027 ba.

Lawal Daura ya ce gwamnatin Tinubu ta tafka kura-kurai da dama, wadanda za su iya kawo karshenta a babban zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262