Tirkashi: Rundunar Sojojin Najeriya Ta Gamu da Gagarumar Matsala da Aka Yi Mata Kutse
- Rundunar sojojin Najeriya ta gano yunkurin kutsawa cikin shafinta ma X ranar Asabar, lamarin da ta bayyana a matsayin matsalar tsaro ta yanar gizo
- An fara wallafa sakonnin da suka shafi memecoin a shafin da misalin ƙarfe 3:50 na yamma, duk da cewa ba a san ko an dawo da cikakken iko ba
- Rundunar ta bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani sako mai shakku, tare da tabbatar da bayanai daga sauran kafafen sadarwarta na hukuma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta ce an yi yunkurin samun damar shiga shafinta na X ba tare da izini ba a ranar Asabar, 29 ga watan Agustan 2026.
Lamarin ya fara bayyana ne bayan aka ga shafin rundunar yana wallafa sakonnin da suka shafi memecoin da misalin ƙarfe 3:50 na yamma.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa yake son dawo da tallafin fetur

Source: Twitter
Sojoji sun fara daukar matakan tsaro
Mukaddashiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Sojin Najeriya, Appolonia Anele, ta ce rundunar ta gano lamarin kuma tana daukarsa a matsayin matsalar tsaro ta yanar gizo.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook na rundunar, Anele ta ce an gano yunkurin samun damar shiga shafin X ba tare da izini ba.
Ta ce nan take aka dauki matakan fasaha da na kariya domin tabbatar da tsaron shafin, hana sake samun damar shiga ba tare da izini ba da kuma kare sahihancin bayanan da ake wallafawa ta kafar.
“Rundunar sojojin Najeriya ta gano kuma tana mayar da martani kan yunkurin samun damar shiga shafinta na X ba tare da izini ba,” in ji ta.
A cewar Anele, rundunar na daukar matakan da suka dace domin tabbatar da cikakken tsaron asusun tare da dawo da ikon gudanar da shi ga jami’an da aka ba izini.
An gargadi jama’a
Rundunar ta shawarci jama’a da kafafen yada labarai su yi taka-tsantsan, tare da yin watsi da duk wani sako da ba a tabbatar da sahihancinsa ba ko kuma wanda ke dauke da bayanan yaudara ko abin zargi daga shafin X din.
Ta kuma bukaci jama’a su rika tabbatar da bayanan da suke samu ta sauran kafafen sadarwa na hukuma na rundunar har sai an warware matsalar gaba daya.
Har zuwa yanzu, ba a tabbatar da ko rundunar ta sake kwato cikakken iko kan shafin X din ba. Sakon karshe da aka wallafa a shafin kafin lamarin ya faru ne.

Source: Twitter
DHQ ma ta fuskanci irin wannan hari
Lamarin ya faru ne kimanin makonni biyu bayan da Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa an kutsa cikin shafin X nata ta hanyar wani hari na yanar gizo.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labaran Tsaro, Samaila Uba, ya fitar a ranar 15 ga Agusta, ya ce DHQ ta dauki matakan fasaha da suka dace domin kare asusun da hana sake samun damar shiga ba tare da izini ba.
Sabbin abubuwan da suka faru sun kara jawo hankali kan bukatar karfafa tsaron yanar gizo na kafafen sadarwar hukumomin tsaro, musamman wadanda ke amfani da su wajen sanar da jama’a muhimman bayanai.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla sojoji huɗu sun jikkata yayin da dakarun Operation Hadin Kai suka dakile wani harin ‘yan ta’adda a garin Kukawa da ke Jihar Borno.
Yayin artabun, an kashe wasu daga cikin maharan, yayin da wasu kuma aka ga suna tserewa da raunukan harbin bindiga.
Asali: Legit.ng

