Yaki Ya Dawo Sabo: Iran Ta kai Hare Hare kan Sojojin Amurka

Yaki Ya Dawo Sabo: Iran Ta kai Hare Hare kan Sojojin Amurka

  • Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin sojin Amurka guda biyu a Jordan
  • Harin na zuwa ne bayan Amurka ta kai hari kan tsibirin Larak a Iran, lamarin da ya sake haddasa musayar hare-hare tsakanin Tehran da Washington
  • Sojojin Jordan sun ce sun tare makamai masu linzami guda takwas da suka kutsa sararin samaniyarta, yayin da ba a samu rahoton jikkata kowa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Bayan Amurka ta kai hari kan tsibirin Larak da ke kudancin Iran a ranar Lahadi, Rundunar IRGC ta sanar da kai wani hari kan sansanonin sojin Amurka a Jordan.

Kamfanonin dillancin labarai na Iran sun ruwaito sanarwar IRGC a ranar Lahadi, inda ta ce an gudanar da harin ne da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi abin da ba za ta taɓa mantawa ba, kuma ba za ta yafe wa Amurka ba

Mojtaba Khamenei da ke shugabantar Iran
Mojtaba Khamenei a hagu da wani jirgin yaki a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta wallafa cewa IRGC ta sanya wa harin suna “Hukunta Azzalumai”, inda ta ce an kai shi kan sansanonin King Hussein da Al Azraq da ke Jordan.

Abin da Iran ta ce ta lalata

IRGC ta yi ikirarin cewa hare-haren sun lalata kayayyakin fasaha da wuraren gyaran jiragen sama, tare da wuraren da ake jibge jiragen yaƙin abokan gaba.

Rundunar ta ce hare-haren sun haifar da gagarumar illa ga wuraren da aka kai wa harin, amma ba ta bayyana cikakken adadin barnar da aka yi ba.

“Tsarin tsaron sararin samaniya ya tare makamai masu linzami guda takwas da suka kutsa sararin samaniyar Masarautar tun wayewar gari a yau, Litinin,”

In ji sojojin Jordan a cikin wata sanarwa.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump yayin wani bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

IRGC ta yi barazanar ƙarin martani

IRGC ta ce hare-haren da Amurka ke kai wa Iran ba za su hana Tehran ci gaba da kare ikonta ba, musamman kan mashigar ruwan Hormuz.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun shammaci ƴan bindiga suna shirin satar kaya a tirela, sun kashe 17

BBC ta wallafa cewa rundunar ta ce duk wani sabon hari da za a kai mata zai fuskanci martani mafi muni daga Iran.

Tehran ta riga ta yi alkawarin mayar da martani kan harin da Amurka ta kai wa Larak Island ranar Lahadi.

Musayar hare-haren na iya sake tayar da rikicin soji tsakanin ƙasashen biyu, a daidai lokacin da Washington ke sauya salon matsin lamba daga hare-haren bama-bamai zuwa dabarun matsin tattalin arziki kan Tehran.

Rasha ta kai hare-hare Ukraine

A wani labarin, mun ruwaito cewa mutane 37 sun mutu, yayin da kusan 400 aka kwashe daga gidajensu bayan wani harin jirgin sama mara matuƙi da Rasha ta kai kan wani wurin ajiyar makamai a kusa da Kyiv.

Harin ya haddasa fashewar harsasai, nakiyoyi da jirage marasa matuƙa da aka ajiye a wurin, lamarin da ya lalata wasu gine-gine da ke kusa, ciki har da wata cibiyar kula da tsofaffi da nakasassu.

Volodymyr Zelensky, ya ce bai kamata a sanya wurin ajiyar makaman a kusa da gidajen jama'a ba, yana mai cewa an fara bincike kan abin da ya kira babban sakaci wajen ajiye abubuwan fashewa kusa da fararen hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng