"Me Ka ke Nufi?" Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani ga Atiku kan Bude Iyakokin Najeriya

"Me Ka ke Nufi?" Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani ga Atiku kan Bude Iyakokin Najeriya

  • Fadar Shugaban Kasa ta tanka wa Atiku Abubakar bayan ya yi alkawarin bude iyakokin Najeriya idan ya ci zaben 2027
  • Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare yce mafi yawan iyakokin Najeriya na kasa a bude suke tun daga watan Maris 2024
  • Fadar ta tambayi Atiku Abubakar wane irin iyaka yake shirin “budewa” idan aka zabe shi a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani kan furucin dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, na cewa zai “bude iyakoki” idan aka zabe shi a 2027.

A cikin wata sanarwa, Sunday Dare, mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan yada labarai da sadarwar jama’a, ya ce Gwamnatin Tarayya ta sanar da sake bude mafi yawan iyakoki tun ranar 14 ga Maris, 2024, kuma ba a sake rufewa ba.

Kara karanta wannan

'Na san ainihin shekarun shugaba Tinubu': Atiku ya ce yana da hujjoji masu ƙarfi

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da hadiminsa, Sunday Dare a fadar Aso Rock Hoto: Sunday Dare
Source: Twitter

Ya ce abu ne mai wahala a fahimci wane irin iyaka tsohon mataimakin shugaban kasar yake son “budewa”, alhali tuni an bude su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sunday Dare ya kuma tunatar da cewa a ranar 14 ga Fabrairu, 2026, Shugaba Tinubu ya bude iyakar Kamba da ke Jihar Kebbi.

Fadar shugaban kasa ta nemi bayani

Sanarwar ta ce ya kamata ’yan Najeriya su san takamaiman irin matakan tsaron iyaka da Atiku yake son cirewa da dalilin da ya sa yake ganin cire su ya zama dole.

Haka zalika ta bukaci Atiku ya kuma fadi matakan da gwamnatinsa za ta dauka wajen dakile ta’addanci, safarar makamai, fasa-kwauri, safarar mutane da sauran nau’o’in manyan laifukan da suka ratsa iyakokin kasashe.

Fadar Shugaban Kasar ta zargi Atiku da iya yin “duk abin da zai ja hankalin masu saukin yaudara a siyasa”, amma ta jaddada cewa bude iyaka ba yana nufin barin iyaka ba tare da kulawa ba.

Kara karanta wannan

Shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya sake gamuwa da cikas gabanin zaben 2027

Muhimman tsaro a iyakokin Najeriya

Ta ce tsarin kula da iyakokin zamani yana da manufar saukaka zirga-zirgar halal, kasuwanci da mu’amalar tattalin arziki, tare da hana miyagu da kungiyoyin ’yan ta’adda amfani da irin wadannan hanyoyi.

Sanarwar ta ce ingantaccen tsarin kula da iyakoki na bukatar hada kula da shige da fice, ayyukan kwastam, musayar bayanan sirri, sa ido, amfani da fasaha da kuma hadin gwiwar hukumomin tsaro.

Fadar ta ce lamarin ya fi muhimmanci ga Najeriya saboda yanayin tsaron arewacin kasar ba zai iya rabuwa da abubuwan da ke faruwa a yankin Sahel da Tafkin Chadi ba.

Ta ce Najeriya tana da iyaka da Nijar, Chadi da Kamaru, yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar matsalolin ta’addanci, tsattsauran ra’ayi da manyan laifukan da suka ratsa iyakokin kasashe.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Fadar ta kara da cewa ya kamata iyakokin Najeriya su kasance a bude ga halastattun kasuwanci da zirga-zirga, amma su kasance cikin tsaro daga ’yan ta’adda da masu aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Atiku ya gano shaidar da ke nuna asalin shekarun Bola Tinubu a duniya

Ya kara da cewa ya kamata a rika sa ido kan iyakokin ta hanyar amfani da fasaha, a tafiyar da su bisa bayanan sirri, sannan a hada su cikin tsarin tsaron kasa da dabarun bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Atiku ya ce shekarun Tinubu 90

Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar ya ce yana da hujjar da ke nun asalin shekarun Bola Tinubu.

Atiku ya bayyana cewa yana da cikakkiyar hujjar da ke nuna Tinubu ya kai shekara 90, sabanin shekarun da yake amfani da su a yanzu watau 74.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262