Babbar Magana: An Yi Kaca Kaca da Shirin Atiku na Bude Iyakoki da Dawo da Tallafin Fetur
- Reno Omokri ya gargadi Najeriya kan sake dawo da tallafin man fetur tare da bude iyakokin kasa baki daya
- Ya ce irin wannan mataki na iya kara safarar man fetur da shigo da kayayyakin haram, tare da raunana tattalin arzikin kasar
- Omokri ya kuma yi gargadin cewa bude iyakokin da ba a fara tabbatar da tsaronsu ba na iya bai wa ’yan ta’adda damar shigo da makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jakadan da aka nada na Najeriya zuwa Mexico, Honduras, Guatemala da Nicaragua, Reno Omokri, ya yi martani kan shirin Atiku na bude iyakokin Najeriya da dawo da tallafin fetur.
Reno Omokri ya yi gargadin cewa sake dawo da tallafin man fetur tare da bude dukkan iyakokin kasa na iya haifar da matsalar safarar man fetur da kuma kara tabarbarewar tsaro.

Kara karanta wannan
Shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya sake gamuwa da cikas gabanin zaben 2027

Source: Facebook
Reno Omokri ya bayyana hakan ne a wata sanarwa ranar Juma’a, 28 ga watan Agustan 2026 da ya sanya a shafinsa na Facebook.
Atiku ya bayyana shirin sake bude iyakokin Najeriya da kasashen makwabta da kuma dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2027.
Ya ce hakan zai taimaka wajen farfado da harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da kasashen makwabta, wadanda ya ce takaita zirga-zirgar kan iyakoki ya shafa.
Omokri ya yi gargadi kan safarar man fetur
Omokri ya ce hada dawo da tallafin man fetur da bude iyakokin kasa baki daya na iya haifar da gagarumar safarar man fetur daga Najeriya zuwa kasashe makwabta.
Ya yi ikirarin cewa a baya, lokacin da Najeriya ke da cikakken tallafin man fetur tare da bude iyakoki, an yi ta fitar da wani kaso mai yawa na man da aka tallafa zuwa kasashen makwabta.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa yake son dawo da tallafin fetur
“Idan aka dawo da tallafin man fetur tare da bude dukkan iyakokin Najeriya lokaci guda, abin da za a yi shi ne bude kofar safarar man fetur mafi girma daga Najeriya zuwa kasashe makwabta,” in ji shi.
Omokri ya ce a wancan lokaci, ana zargin ana safarar lita miliyan 25 na man fetur a kullum daga cikin adadin lita miliyan 66.1 da ake tallafawa a kowace rana.
Ya ambaci matsalar shigo da shinkafa da kaji
Jakadan ya kuma yi ikirarin cewa bude iyakoki ya taba bai wa masu safarar kayayyaki damar shigo da shinkafa da kaji daga kasashe makwabta zuwa Najeriya.
A cewarsa, hakan ya taimaka wajen raunana manoman shinkafa da masu kiwon kaji na cikin gida, saboda kayayyakin da ake shigowa da su ta haramtacciyar hanya suna shiga kasuwa da farashi mai rahusa.
Omokri ya ce sakamakon hakan ya hada da matsin lamba kan ajiyar kudaden waje da darajar Naira, da kuma matsalolin da manoma da masana'antun cikin gida suka fuskanta.
Ya kuma yi ikirarin cewa kungiyar Rice Processors Association of Nigeria (RIPAN) ta bayyana cewa safarar shinkafa ta tilasta wa wasu manyan masana'antun sarrafa shinkafa rufe ayyukansu.
Ya ce za a rika shigo da makamai
Omokri ya kuma ce bude iyakokin kasa ba tare da ingantaccen tsaro ba na iya bai wa ’yan ta’adda da ’yan bindiga damar shigo da kananan makamai da harsasai cikin Najeriya.
Ya ce idan aka bude iyakokin gaba daya ba tare da kara yawan jami’an tsaro da na kwastam da shige da fice ba, hukumomin tsaron iyakokin za su iya kasa kula da yawan zirga-zirgar da za ta biyo baya.
“Bude iyakokin Najeriya ba tare da fara tabbatar da tsaronsu ba na jefa tsaron Najeriya da tattalin arzikinta cikin hadari,” in ji shi.

Source: Twitter
Atiku ya fadi shekarun Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ikirarin cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai shekara 90 a duniya.
Atiku ya bayyana cewa yana da cikakkiyar hujjar da ke nuna Tinubu ya kai shekara 90, sabanin shekarun da yake amfani da su a yanzu watau 74.
Asali: Legit.ng
