Wata Sabuwa: A Dauko Hoton Shekaru 60 da Suka Gabata don Kare Yawan Shekarun Tinubu

Wata Sabuwa: A Dauko Hoton Shekaru 60 da Suka Gabata don Kare Yawan Shekarun Tinubu

  • Atiku Abubakar ya kalubalanci shekarun Bola Tinubu, inda ya ce yana da shaidar da ke nuna shugaban Najeriya ya kai shekaru 90
  • Reno Omokri ya mayar da martani, inda ya nemi Dele Momodu ya tabbatar da sahihancin hoton da aka ce an dauka tare da Tinubu a Landan a 1996
  • Omokri ya ce idan Tinubu yana da shekaru 90 a 2026, to zai kasance yana da shekaru 60 a lokacin da aka dauki hoton

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Reno Omokri, jakadan Najeriya mai jiran aiki a Mexico, Honduras, Guatemala da Nicaragua, ya kalubalanci ikirarin Atiku Abubakar na cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da shekaru 90.

Omokri ya kuma kalubalanci dan jarida kuma mawallafi, Dele Momodu, da ya tabbatar da sahihancin wani hoto da ya ce an dauke shi tare da Tinubu a Landan a shekarar 1996.

Kara karanta wannan

'Na san ainihin shekarun shugaba Tinubu': Atiku ya ce yana da hujjoji masu ƙarfi

Reno Omokri.
Jakadan Najeriya mai jiran gado, Reno Omokri Hoto: Reno Omokri
Source: Getty Images

Jakadan ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma'a, 28 ga watan Agusta, 2026.

Wannan martani ya biyo bayan wata hira da Atiku, dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027, ya yi da BBC, inda ya yi ikirarin cewa Tinubu yana da shekaru 90 tare da cewa yana da shaidar tabbatar da hakan a kotu.

Omokri ya ƙalubalanci ikararin Atiku

Da yake mayar da martani kan ikirarin, Omokri ya wallafa wani hoto da ake zargin yana nuna Tinubu tare da Momodu a Landan a shekarar 1996.

Ya ce hoton na sanya ayar tambaya kan ikirarin cewa shugaban kasar yana da shekaru 90.

“Wannan hoto ne na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Dele Momodu da aka dauka a Landan a 1996. Idan da gaske Asiwaju yana da shekaru 90, kamar yadda ya yi, to Dele Momodu dole ne ya kasance yana da shekaru sama da 80,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Atiku ya gano shaidar da ke nuna asalin shekarun Bola Tinubu a duniya

Omokri ya ce Momodu yana raye kuma zai iya tabbatar da sahihancin hoton, da kuma lokacin da wurin da aka dauke shi.

Omokri ya kafa hujja da hoto

Ya kara da tambayar ko Tinubu yana kama da mutum mai shekaru 60 a hoton, yana mai cewa idan shugaban kasar yana da shekaru 90 a 2026, to zai kasance yana da shekaru 60 lokacin da aka dauki hoton shekaru 30 da suka gabata.

Omokri ya bukaci ’yan Najeriya da sauran mutanen duniya su duba hoton da kansu, inda ya tambaya ko mutumin da ke gefen dama yana kama da mai shekaru 60 ko ma 50.

Nawa ne shekarun Tinubu?

A cewar bayanan da aka bayyana a hukumance, Bola Tinubu yana da shekaru 74, bayan an haife shi a ranar 29 ga Maris, 1952.

Shugaban kasar ya taba fuskantar tambayoyi da cece-kuce kan shekarunsa da kuma bayanan karatunsa, amma ya ci gaba da tsayawa kan bayanan da aka bayyana game da tarihinsa.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da hoton Bola Tinubu da Dele Momodu Hoto: Reno Omokri
Source: Facebook

Atiku ya yi alkwarin dawo da tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin ADC ya sha alwashin magance matsalar tsaro.

‘Dan takaran jam’iyyar hamayya ta ADC ya ce ba zai dauki fiye da shekara guda a fadar Aso Rock Villa bai magance matsalar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262